Kan rike mai asusun albashi, Soja ya bindige kwamandansa har lahira
Wani Sojan Najeriya dake 202 Bataliya dake Bama jihar Borno ya bindige Laftana kwamandarsa, Bakaka Ngorgo, kan rashin bashi daman tafiya domin magance wasu matsalolin da suka tattari rashin samun albashinsa na tsawon watanni takwas.
Soaj wanda aka sakaye sunansa ya budwa shugabansa wuta ne yayinda magana a wayar salula ranar Laraba a hedkwatar.
Ba tare da bata lokaci ba aka damke Sojan yayinda aka garzaya da agwar hafsan da ya kashe zuwa asibitin 7div.
Harbin ya tayarwa Sojoji da Hafsoshin 202 Bataliya hankali.
Majiyoyin jaridar Punch a gidan Soja sun bayyana cewa an daskarar da asusun Sojan ne sakamakon zuwa hutun da yayi ba tare da izini ba.
An ce yayinda ya dawo, ya bukaci marigayin ya bashi damar zuwa magance matsalar, amma Ngorgi ya hana shi.
Abubuwa sun yi muni lokacin da Sojan ya budewa hafsan wuta har lahira.
A cewar rahotanni, Ngorgi bai dade da aure ba.
KU KARANTA: Jerin jihohin Arewan da aka hana bukukuwan Sallah
Wata majiya tace: "Abin takaicin ya auku ne a 202 Batallion Bama, lokacin da Soja ya harbe mataimakin kwamanda. Sun samu sabani ne kan wani lamari."
"Bayan haka, Hafsan ya hana Sojan damar fita magance matsalarsa bayan wtaanni takwas babu albashi da alawus. Soja ya tafi hutun watanni shida ba tare da izini ba."
"Saboda haka ranar Laraba, ya kara da carbin harsasai 30 kan Hafsan. An damkeshi ba tare da bata lokaci ba."
Kakakin hukumar Sojin Najeriya, Kanar Sagir Musa, ya tabbatar da hakan kuma ya ce an kaddamar da bincike kan lamarin.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng