Aljannar duniya: Bidiyon katafaren gidan Floyd Mayweather mai darajar N3.8bn
- Fitaccen dan wasan damben nan, Floyd Mayweather ya mallaki fiye da $1,000,000,000 yana harkarsa ta dambe
- Bidiyoyin kasaitaccen gidan da dan damben mai shekaru 43 ya mallaka, wanda akalla ya kai £8,000,000, ya kayatar da mabiyansa
- Cikin gidan akwai tafka-tafkan wuraren wanka 2 da katon garejin motocinsa cike makil da tsadaddun motoci irin na zamani
Mayweather ya bayyana bidiyon kasaitaccen gidansa na kimanin £8,000,000, wanda yake da wasu manya-manyan wuraren wanka tare da garejin motocin da a kalla zai dauki motoci 20.
Bidiyon gidan sun bayyana a kafafen sada zumuntar zamani bayan wani Devin Haney mai shekaru 21 ya kai ziyara katafaren gidan dake Las Vegas, ya dauka kuma ya wallafa a kafafen sada zumuntar zamani, kamar yadda SunSport suka ruwaito.
Haney ya zagaye gidan dan damben mai shekaru 43. A bidiyon farko, an ga wurin ajiyar takalmansa. Bidiyon ya bayyana wasu kofofin kwalba masu kayatarwa kafin a koma wuraren garejin motarsa.
KU KARANTA: Matashiya mai shekaru 18 ta mutu a masaukin bakin gwamnan Yobe, mutum 4 sun shiga hannu
Mayweather ya samu fiye da $1,000,000,000 lokacin da yake dambe, kuma ya yi amfani da fiye da £20,000,000 wurin siyan kasaitattun motoci.
Cikin motocinsa akwai Rolls-Royce wacce tsadarta ta kai £3,000,000 da kuma Bugatti Veyron guda 4, kuma ko wacce a kalla ta kai tsadar £1,700,000.
A bidiyon an nuna wuraren wanka masu kayatarwa, na ciki da waje guda 2.
KU KARANTA: 'Yan bindiga sun kai hari wani kamfanin shinkafa a Kano, sun kashe mutum 1
A wani labarai na daban, Jaruma Rahama Sadau ta samu damar ganawa da kwamishinan fina-finai na Quebec da ke kasar Canada.
Kamar yadda jarumar ta wallafa a shafinta na Instagram, ta sanar da cewa ta samu ganawa da Hans Fraikin a yayin da ta kai ziyara daular larabawa.
Kamar yadda ta wallafa, "Dole ne in ce 2021 ta fara da farin ciki. A yayin hutu na, shakawata da abokai, ziyara da sauransu da nayi a UAE, na samu damar ganawa da Hans Fraikin, kwamishinan fina-finai na Quebec ta kasar Canada."
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng