Matashiya mai shekaru 18 ta mutu a masaukin bakin gwamnan Yobe, mutum 4 sun shiga hannu

Matashiya mai shekaru 18 ta mutu a masaukin bakin gwamnan Yobe, mutum 4 sun shiga hannu

- 'Yan sanda jihar Yobe sun damke wasu mutum 4 da ake zargi da hannu a mutuwar matashiya mai shekaru 18

- Wani mutum ya kira 'yan sanda tare da sanar musu ya kwana da matashiya mai shekaru 18 amma ta mutu da safe

- Kamar yadda yace, ya kwana da matashiyar amma sai da safe ya gane cewa a bige take wanda daga baya ta mutu

Rundunar 'yan sandan jihar Yobe ta cafke wasu mutum 4 da ake zargi da hannu a mutuwar wata budurwa mai shekaru 18 a masaukin bakin gwamnatin jihar Yobe da ke Damaturu.

Premium Times ta gano cewa lamarin ya faru ne a ranar Alhamis. 'Yan sandan sun damke mutanen da ake zargi da hannu.

Majiya daga rundunar 'yan sandan ta ce babban wanda ake zargin shine wani mutum mai suna Al-bash Yahaya Ibrahim tare da wasu mutum uku.

Matashiya mai shekaru 18 ta mutu a masaukin bakin gwamnan Yobe, mutum 4 sun shiga hannu
Matashiya mai shekaru 18 ta mutu a masaukin bakin gwamnan Yobe, mutum 4 sun shiga hannu. Hoto daga @Premiumtimes
Source: Twitter

KU KARANTA: Nasara daga Allah: Bidiyon sojin sama suna ragargaza shugabannin Boko Haram

An mika gawar matashiyar asibitin kwararru na jihar Yobe da ke Damaturu domin gano abinda ya kasheta.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar, Dungus Abdulkarim, ya tabbatar da aukuwar lamarin.

"An kama mutum hudu da ake zargi da kisan kai," yace.

Kamar yadda yace, "Dukkan abubuwan da ake zarginsu da shi za su bayyana ne bayan an gano musababin mutuwar yarinyar."

"Wani Dr Al-Bash Ibrahim Yahaya ya sanar da 'yan sanda cewa ya kwana da matashiyar kuma ta rasu a dakinsa.

"Ya sanar da 'yan sanda cewa shi bako ne a gidan gwamnatin jihar Yobe kuma ya bukaci da a kawo mishi matashiya wacce za ta taya shi kwana. Ya kwana da ita amma sai da safe ya gane cewa a bige take.

"Ya ce ta fara wasu abubuwa tare da kakkarwa. Binciken farko ya nuna a bige take da kwayoyi," Dungus yace.

KU KARANTA: Matashi ya bayyana yadda budurwarsa ta rabu da shi saboda ya ki fara 'Yahoo'

"Dr Al-bash ya kira wadanda suka kawo mishi ita kuma ya sanar da su abinda ke faruwa. Sun fara bata madarar ruwa wanda kafin kace kwabo ta ce ga garinku," Ya kara da cewa.

Ya tabbatar da cewa a halin yanzu dai ana bincike.

Premium Times ta gano cewa yarinyar ta kammala makarantar sakandire a 2020.

A wani labari na daban, an halaka mutane uku yayin da wani daya ya samu rauni a lokacin da wasu mayakan ta'addanci da ake zargin 'yan Boko Haram ne suka kai hari kusa da Maiduguri, babban birnin jihar Borno a daren Laraba, majiyoyi suka sanar.

An gano cewa 'yan ta'addan sun tsinkayi kauyen Ngunari kusa da Yankin Moromti wurin karfe 10:30 na dare a karamar hukumar Konduga inda suka kashe mutum uku.

Abubakar Kulima jami'in tsaro ne daga cikin jami'an hadin guiwa na CJTF. Ya ce maharan sun dinga harbe-harbe kuma sun yi awon gaba da dabbobi a kauyen, Daily Trust ta ruwaito.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel