Allah ya yi wa tsohon gwamnan Kano, Isah Kontagora, rasuwa
- Allah ya yi wa Kanal Aminu Isah Kontagora mai ritaya rasuwa
- Sakataren gwamnatin jihar Neja ne ya fitar da sanarwar rasuwar a yau Litinin
- Marigayin ya mulki jihohin Binuwai da Kano a yayin mulkin soja a Najeriya
Allah ya karba ran tsohon gwamnan jihar Kano, Aminu Isah Kontagora.
An tabbatar da rasuwar tsohon gwamnan bayan sakataren gwamnatin Neja ya bada sanarwar a wata takardar da ya fitar.
Marigayi Aminu Isah Kontagora ya rasu bayan gajeriyar rashin lafiya da yayi fama da ita a garin Abuja.
A lokacin rayuwarsa, ya taba mulkar jihohin Binuwai da Kano a yayin mulkin soja.
An haifa marigayin a shekarar 1956 kuma ya mulki jihar Kano daga watan Satumban 1998 zuwa watan Mayun 1999.
Sojan mai mukamin Kanal ya mika wa farar hula ragamar mulki a shekarar 1999 zamanin mulkin shugaban kasa Janar Abdulsalami Abubakar.
Kamar yadda takardar sanarwar da sakataren gwamnatin Neja ya fitar, ya ce marigayin kamilin soja ne wanda za a dinga tunawa da shi saboda gudumawar da ya bada wurin cigaban jihohin Binuwai da Kano.
Tsohon gogaggen dan siyasan ya rike manyan mukamai kafin rasuwarsa.
KU KARANTA: Boko Haram sun kashe mutum 3, sun yi awon gaba da dabbobi a kusa da Maiduguri
A wani labari na daban, rundunar 'yan sandan jihar Yobe ta cafke wasu mutum 4 da ake zargi da hannu a mutuwar wata budurwa mai shekaru 18 a masaukin bakin gwamnatin jihar Yobe da ke Damaturu.
Premium Times ta gano cewa lamarin ya faru ne a ranar Alhamis. 'Yan sandan sun damke mutanen da ake zargi da hannu.
Majiya daga rundunar 'yan sandan ta ce babban wanda ake zargin shine wani mutum mai suna Al-bash Yahaya Ibrahim tare da wasu mutum uku.
An mika gawar matashiyar asibitin kwararru na jihar Yobe da ke Damaturu domin gano abinda ya kasheta.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng