Matashi ya siya mota a matsayin alamar dogaro da kai, ya ce baya son raini daga mahaifinsa

Matashi ya siya mota a matsayin alamar dogaro da kai, ya ce baya son raini daga mahaifinsa

- Matashi mai shekaru 19 ya siya wa kansa sabuwar mota dal irin wacce mahaifinsa ya ba shi kyauta

- Matashin ya ce dole ce ta sa yayi hakan saboda maganar da mahaifinsa yake yi kullum a kan motar

- A tsarin shi na nan gaba, ya ce yana kokarin ganin ya tsayu da kansa ba tare da dogaro da kowa ba nan babu dadewa

Wani matashi mai shekaru 19 mai suna @oustsucced a Twitter ya nuna cewa tabbas zai iya kula da kanshi kuma zai iya dogaro da kafafunsa.

A wata wallafa da yayi a ranar Alhamis, 31 ga watan Disamban 2020, matashin ya ce motarsa ta farko mahaifinsa ya bashi kyauta.

Ya ce tun bayan da mahaifinsa ya bashi kyautar, ya dinga mishi maganganu a kan hakan tare da gori. Matashin ya ce ya gaji da lamarin don haka ya je ya nemi kudi ya siya motar irin wacce mahaifinsa ya siya masa shima ya siya.

KU KARANTA: Nasara daga Allah: Bidiyon sojin sama suna ragargaza shugabannin Boko Haram

Matashi ya siya mota a matsayin alamar dogaro da kai, ya ce baya son raini daga kowa
Matashi ya siya mota a matsayin alamar dogaro da kai, ya ce baya son raini daga kowa. Hoto daga @Outsucced
Source: Twitter

@outsucced ya ce ya siya irin motar kuma ya sanar da jama'a cewa ba zai lamunci wulakanci ba kowanne iri ne.

Ya kara da cewa abu na gaba da zai fara kokarin yi shine tara kudi ya samu gidan zama nashi shi kadai.

KU KARANTA: Da duminsa: Kakakin majalisa Pelosi ta bukaci a tsige Donald Trump

A wani labari na daban, wani matashi dan Najeriya ya bar jama'a a kafar sada zumuntar zamani cike da mamaki bayan ya bada labarin rabuwarsa da tsohuwar budurwarsa.

Ya ce ta bashi na'ura mai kwakwalwa kyauta a ranar zagayowar haihuwarsa domin ya fara damfara a yanar gizo.

Kamar yadda ya bayyana a labarin, ta ce bata jin dadin albashinsa domin baya isarsu. Don haka ta bashi kyautar ne don ya shiga gungun wasu masu damfarar yanar gizo.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel