FG: Adadin allurar rigakafin korona da kowacce Jiha za ta samu
- Hukumar kula da harkar lafiya a matakin farko (NPHCD) ta sanar da cewa nan bada dadewa za'a fara rabawa jihohi alluran rigakafi
- Gwamnatin tarayya ta ce zata yi la'akari da alkaluman masu kamuwa da cutar wajen rabon alluran rigakafin
- A cewar NPHCD, Jihar Kano za ta samu alluran rigakafi mafi yawa, 3,557, a rukunin farko na rabon
Hukumar kula da lafiya a matakin farko (NPHCD) ta sanar da cewa gwamnatin tarayya ta fitar da jadawalin rabon alluran rigakafin korona ga jihohi.
Hukumar kula da cututtuka masu yaduwa a kasa (NCDC) ta ce za'a duba alkaluman masu kamuwa da kwayar cutar korona a jihohi wajen rabon alluran rigakafin.
An samu adadin sabbin mutane 1,585 da suka sake kamuwa da kwayar cutar korona a Nigeria a ranar 9 ga watan Janairu.
NCDC ta ce adadin wadanda suka kamu da kwayar cutar korona a Nigeria ya tashi daga mutum 97,478 a ranar 8 ga watan Janairu, zuwa mutum 99,063 a ranar Asabar, 9 ga watan Janairu.
KARANTA: Buhari da Osinbajo zasu karbi allurar rigakafin korona, za'a nuna a talabijin kowa ya gani
Ga adadin alluran rigakafin da kowacce Jiha zata samu kamar yadda NCDC ta wallafa;
1. Kano: 3,557
2. Lagos: 3,131
3. Katsina: 2,361
4. Kaduna: 2,074
5. Bauchi: 1,900
KARANTA: Hatsarin mota ya yi sanadiyyar rasuwar yarima Nuhu, matarsa, da 'ya'yansu hudu a hanyar Abuja
6. Oyo: 1,848
7. Rivers: 1,766
8. Jigawa: 1,712
9. Niger: 1,558
10. Ogun: 1,473
11. Sokoto: 1,468
12. Benue: 1,423
13. Borno: 1,416
14. Anambra: 1,379
15. Zamfara: 1,336
16. Delta: 1,306
17. Kebbi: 1,268
18. Imo, 1,267
19. Ondo: 1,228
20. Akwa Ibom: 1,161
21. Adamawa: 1,129
22. Edo: 1,104
23. Plateau: 1,089
24. Enugu: 1,088
25. Osun: 1,032
26. Kogi: 1,030
27. Cross River: 1,023
28. Abia: 955
29. Gombe: 908
30. Yobe: 842
31. Ekiti: 830
32. Taraba: 830
33. Kwara: 815
34. Ebonyi: 747
35. Bayelsa: 589
36. FCT, 695
Gwamnati ta ce tana fatan yi wa kaso 40% na 'yan Nigeria alluran rigakafin a rukunin farko a cikin shekarar 2021.
Ana saka ran yi wa karin kaso 30% na 'yan Nigeria allurar a cikin shekarar 2022.
Kazalika, NCDC ta sanar da cewa gwamnatin tarayya na cigaba da farauto allurar rigakafin daga sauran kasashen duniya da suka hada da Russia.
A ranar 5 ga watan Janairu ne Legit.ng ta rawaito cewa a karo na farko cikin sabuwar shekarar 2021, shugaban kungiyar Boko Haram, Abubakar Shekau, ya saki sabon faifan sakon.
A cikin sabon sakon faifan sautin muryar, Shekau ya yi gargadi na musamman ga babban malamin addinin Islama, Sheikh Dakta Ahmad Gumi, kamar yadda Jaridar Daily Nigerian ta sanar.
Shekau ya gargadi Gumi akan alakanta kungiyar Boko Haram da Fulanin da ke yin garkuwa da mutane domin neman kudin fansa.
Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng