PDP ba ta da sauran wani tasiri a Nigeria; Tsohon gwamnan jam'iyyar daga arewa ya tsallaka APC

PDP ba ta da sauran wani tasiri a Nigeria; Tsohon gwamnan jam'iyyar daga arewa ya tsallaka APC

- Bala Ngilari, tsohon gwamnan jihar Adamawa, ya ce jam'iyyar PDP ta gama mutuwa kuma a 2023 za'a binneta

- Tsohon gwamnan ya yi takarar kujerar sanata a zaben 2019 a karkashin inuwar jam'iyyar PDP kafin ya koma APC a 2020

- Ngilari ya ce duk wani kishin kasa a halin yanzu zai fi son a alakanta shi da jam'iyyar APC fiye da jam'iyyar PDP

Tsohon gwamnan jihar Adamawa, Bala Ngilari, ya ce PDP ba ta da wani sauran katabus a Nigeria tare da bayyana cewa jam'iyyar ta mutu.

Ngilari ya bayyana hakan ne ranar Asabar yayin da ya halarci taron masu ruwa tsaki na jam'iyyar APC a Yola, babban birnin jihar Adamawa, kamar yadda Punch ta rawaito.

Tsohon gwamnan ya nemi takarar kujerar Sanata a karkashin inuwar jam'iyyar PDP a zaben shekarar 2019 kafin daga bisani ya koma APC a 2020.

"Daya daga cikin dalilan da suka sa na bar PDP shine saboda jam'iyyar ta durkushe, na takaice magana; jam'iyyar PDP ta mutu kuma a 2023 za'a binneta.

KARANTA: Hatsarin mota ya yi sanadiyyar rasuwar yarima Nuhu, matarsa, da 'ya'yansu hudu a hanyar Abuja

"Dalili na biyu shine bana ganin jam'iyyar PDP a matsayin wacce za ta inganta Nigeria fiye da APC.

PDP ba ta da sauran wani tasiri a Nigeria; Tsohon gwamnan jam'iyyar daga arewa ya tsallaka APC
PDP ba ta da sauran wani tasiri a Nigeria; Tsohon gwamnan jam'iyyar daga arewa ya tsallaka APC
Source: Facebook

"Rigingimun da ke cikin jam'iyyar sune zasu kai mambobinta ga makabarta mu kuma mu taimaka wajen binnesu."

KARANTA: Kano: 'Yan bindiga sun yi harbe-harbe a kan titin zuwa gidan Zoo

"Gara na shiga jam'iyyar APC saboda na fi gamsuwa da manufofi da tsare-tsarensu musamman ga makomar Nigeria a nan gaba," a cewar Ngilari.

Tsohon gwamnan ya kara da cewa duk wani mai kishin kasa a yanzu zai fi son a alakanta shi da jam'iyyar APC.

A baya Legit.ng Hausa ta rawaito cewa fadar shugaban kasa ta yi raddi tare da yi wa jam'iyyar adawa ta PDP kaca-kaca.

A wani jawabi da Garba Shehu, kakakin shugaban kasa, ya fitar, fadar shugaba kasa ta ce duk wani sauran tasiri da PDP keda shi ya kare saboda ta zama jami'ar karya, kamar yadda Daily Trust ta rawaito.

A cewar fafa shugaban kasa, jam'iyyar PDP ba ta yi komai ba a tsawon mulkinta na shekaru goma sha shidda bayan assasa cin hanci da rashawa.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel