Manyan garkuwa da mutane guda 10 da suka shiga tarihi a arewacin Nigeria

Manyan garkuwa da mutane guda 10 da suka shiga tarihi a arewacin Nigeria

- Akwai hare-haren ƙwamushe mutane da yawa da akayi a Najeriya wanda ba za'a taɓa mantawa da su ba

- A shekarun da suka gabata, Najeriya ta sha fama da hare-haren ta'addanci daga ƙungiyoyin 'yan ta'adda da ƴan bindiga

- Rahoton da SB Morgen suka rawaito ya nuna cewa daga shekarar 2011 zuwa 2020, an biya sama da miliyan $18 (Biliyan₦6.9) a matsayin kuɗin fansar waɗanda aka sace a Nigeria

Wani Rahoto ya bayyana cewa, daga shekarar 2016 zuwa 2020, an biya miliyan $11 (₦4.2bn),wanda ya ke nuni da maida harkar ƙwanushe mutane a matsayin kasuwanci, kamar yadda Punch ta wallafa.

Rahotonmu zai kawo muku ƙwamushe 10 da ba za'a manta da su ba a tarihin Najeriya, farawa da na makarantar maza ta Ƙanƙara jihar Katsina.

1. Satar ɗalibai maza a ƙanƙara.

Da yammacin 11 ga watan Disamba, 2020,wasu gungun ƴaɓ bindiga a babura suka mamaye Makarantar Sakandiren Kimiyya ta Maza,Ƙanƙara jihar Katsina,wadda ke ɗauke da sama da ɗalibai 800 a cikinta.

Lokacin da aka ƙaddamar da harin, Shugaban ƙasa, Muhammad Buhari ya na cikin jihar Katsina, a garinsu na Daura.

2. Sace Ƴan matan Chibok

Wannan shima ƙwamushe ne wanda ba za'a manta da shi ba a tarihi ba, wanda ba iya Najeriya ya girgiza ba, hatta duniya sai da ta jijjiga da faruwar lamarin.

An dai sace ƴan mata sama 200 daga makarantar Sakandiren Mata da ke Chibok, Jihar Borno a ranar 14 ga watan Afrilun shekarar 2014.

KARANTA: Yuana: Shekau yana cikin rashin lafiya mai tsanani, yana neman addu'ar Kiristoci da Musulman Nigeria

Wannan ƙwamushen da ƴan Boko Haram suka yi ya sha caccaka sosai daga ƙungiyoyin duniya daban daban.

Faruwar lamarin ya shafawa Gwamnatin Shugaba Goodluck Jonathan baƙin fenti.

Manyan garkuwa da mutane guda 10 da suka shiga tarihi a arewacin Nigeria
Manyan garkuwa da mutane guda 10 da suka shiga tarihi a arewacin Nigeria @Punch
Source: Twitter

3. Sace Ƴan matan Dapchi

Shekaru huɗu bayan sace ƴan matan Chibok aka sake kwatanta irinsa a garin Dapchi, Jihar Yobe.

Gwamnan jihar Yobe na lokacin, Ibrahim Gaidam, ya ɗora alhakin faruwar lamarin akan sojojin Najeriya sakamakon janye shingen binciken sojoji da suka yi daga garin.

KARANTA: Kano: 'Yan bindiga sun yi harbe-harbe a kan titin zuwa gidan Zoo

Bayan wata guda,an sako yan matan duka ban guda ɗaya tal, wata yarinya Kirista mai suna Leah Sharibu, wacce aka ƙi sakinta sakamakon ƙin barin addininta zuwa musulunci.

4. Sace Malaman Jami'ar Maiduguri UNIMAID

Wannan yana ɗaya daga cikin abubuwan da suka jijjiga ƙasar nan.

A watan Yulin shekarar 2017, ƴan ta'addan Boko Haram suka kai hari kan tawagar malaman jami'ar da suke aiki ƙarƙashin masarrafar man fetur din Najeriya (NNPC) wanda suke ƙoƙarin gano man fetur a Kwarin Lake Chad.

Tawagar ta haɗar da Ma'aikatan UNIMAID, mambobin ƙungiiyar sa kai ta civilian JTF da jami'an JTF.

Ƴan ta'addan sun kashe ma'aikatan jami'ar biyar, kana suka ƙwamushe huɗu daga cikin malaman, kamar yadda ƙungiyar malaman jami'ar reshen UNIMAID ta tabbatar.

5. Sace ma'aikatan ceto da tallafi da ƴan Boko Haram su ka yi

Sakamakon fusata da ƙungiyar Boko Haram ta yi yadda ƙungiyoyin ceto ke tallafawa waɗanda abin ya shafa.

Ƴan ta'addar Boko Haram a ranar 18 ga watan Yuli,2019 sun ƙwamushe ma'aikatan ceto shida akan hanyar su ta zuwa kai tallafi Damask,Jihar Borno.

6. Sacewa da kuma kashe ma'aikatan Red Cross (ICRC)

Ɗaya daga cikin abubuwan jimami shine ƙwamushe ma'aikatan ceto na ƙungiyar ICRC(Red Cross) tare da ma'aikacin jinya guda ɗaya a ranar 18 ga watan Maris 2018,a ƙaramar hukumar Kala-Balge ta jihar Borno.

Sai dai Boko Haram ta kashe ɗayansu a watan Satumba, ɗayan kuma a watan Oktoba.

7. Sace ɗaliban jami'ar Ahmadu Bello Zaria

A wani hari da aka kaddamar kan al-ummar jami'ar a ranar 15 ga watan Nuwamba, 2020, an ƙwamushe ɗalibai 9 na jami'ar Ahmadu Bello Zariya, Jihar Kaduna, akan babban titin Abuja zuwa Kaduna.

Ɗaliban suna kan hanyar su ta zuwa Legas don halartar wani taro da aka Shirya a French Language Village dake Badagry Legas lokacin da lamarin ya afku.

Ɗaya daga cikin ɗaliban ya kuɓuto daga hannun ƴan bindigar da raunin alburushi,inda ya ce ƴan bindigar na bukatar Miliyan ₦30 daga ahalin kowanne daga cikin waɗanda aka sace.

Sai dai sun yi ragi zuwa miliyan ɗaya akan kowanne ɗalibi.

8. Ƙwamushe ma'aikatan jinƙai huɗu a jihar Borno

A cikin wani hari da ba'a tsammaci afkuwarsa ba,ƴan ta'addan Boko Haram sun ƙwamushe wasu ma'aikatan jinƙai da kuma jami'in tsaro daga ma'aikatu daban daban.

An yi nasarar ƙwamushe su ne ya yin wani harin kwanton ɓauna akan hanyarsu ta zuwa birnin Maidugurin jihar Borno.

Sai dai bayan wata guda da ƙwamushe ma'aikatan, ƴan ta'addan sun kashe su gabaɗaya,kamar yadda ofishin majalisar ɗinkin duniya mai kula da harkokin jinkai ya tabbatar.

A ranar Lahadi ne Legit.ng ta rawaito cewa shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya ce ko kadan ba ya jin dadin yadda 'yan ta'adda ke kashe jama'a a Nigeria

A cewar Buhari, gwamnatinsa ta yi wasu tsare-tsare domin kawo karshen kungiyar Boko haram a cikin shekarar 2021.

Buhari ya lissafa wasu dalilai hudu da zasu bawa gwamnatinsa damar ganin baya kungiyar Boko Haram a 2021

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel