Kano: 'Yan bindiga sun yi harbe-harbe a kan titin zuwa gidan Zoo

Kano: 'Yan bindiga sun yi harbe-harbe a kan titin zuwa gidan Zoo

- Wasu 'yan bindiga sun firgita jama'a bayan sun yi harbe-harbe kafin daga daga bisani su kwace wata mota

- 'Yan bindigar sun fito da mai motar ta karfin tuwo sannan suka harbe shi kafin su gudu da ita

- Kakakin rundunr 'yan sandan jihr Kano, DSP Abdullahi Kiyawa, ya ce an samu motar bayan bin sahun 'yan ta'ddar

Wasu 'yan bindiga sun yi harbe-harbe tare da tarwatsa jama'a a daidai katafaren shagon Ado Bayero Mall da ke kan titin zuwa gidan Zoo a birnin Kano.

Freedom Radio ta rawaito cewa lamarin ya faru ne da misalin karfe goma na daren ranar Asabar.

A cewar rahoton da Freedom Radio ta wallafa, 'yan bindigar sun yi harbe-harbe a sararin samaniya, lamarin da ya saka jama'a gudun neman mafaka.

'Yan bindigar sun nufi wata inda suka fito da mutumin da ke ciki tare da harbinsa nan take kafin su gudu da motar.

KARANTA: Ina kisa ne domin kawai na samu kudin shan giya da shagwaba budurwata - Matashi Tajudeen

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Kano, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya tabbatar wa da Freedom Radio faruwar lamarin tare da sanar da cewa sun kai mutumin da aka harba asibiti.

Kano: 'Yan bindiga sun yi harbe-harbe a kan titin zuwa gidan Zoo
Kano: 'Yan bindiga sun yi harbe-harbe a kan titin zuwa gidan Zoo
Source: Facebook

Kazalika, ya bayyana cewa 'yan sanda sun dauko motar da 'yan bindigar suka kwata bayan sun gudu sun barta sakamakon matsin lamba daga jami'an 'yan sanda da ke kokarin cin musu.

A ranar Alhamis, 7 ga watan Janairu, ne Legit.ng ta rawaito cewa a kalla sinadarai masu fashewa guda biyu aka gano a birnin Washington DC sakamakon rikicin da ya barke ranar Laraba, kamar yadda Premium Times ta samu rahotanni daga kasar Amurka.

KARANTA: Adadin mutanen da kowacce jiha ta rasa sakamakon ayyukan ta'addanci a 2020

Kazalika, jaridar Punch ta rawaito cewa majiyarta a kasar Amurka ta tabbatar mata da mutuwar wata mata da sanarwa ta bayyana cewa ta samu rauni sakamakon harbin bindiga.

Rikici ya barke a Capitol, Washington, bayan magoya bayan shugaba Trump sun yi kutse domin dakatar da tabbatar da nasarar da Joe Biden ya samu a zaben da aka yi a watan Nuwamba, 2020.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel