Hotunan auren bazawara mai shekaru 50 da bazawari mai shekaru 60 sun kayatar
- Kyawawan hotunan bazawara mai shekaru 50 da bazawari mai shekaru 60 da suka yi aure ya yadu a kafafen sada zumunta
- Amarya mai suna Bose da angonta Patrick sun yi aure tare da shirya gagagrumin biki tamkar yara masu jini a jika
- Bose ta sanar da cewa babban dan Patrick ne ya hada su a Ingila wanda daga hakan soyayya ta kullu
Wasu sabbin aure wadanda matar ke cikin shekarunta na hamsin yayin da mijin ke cikin shekarunsa na sittin sun janyo cece-kuce a kafafen sada zumunta.
Bose da Patrick sun kasance dattawa kuma sun daura aure a kayataccen bikin da suka shirya wanda 'yan uwa da abokan arziki suka samu halarta, The Nation ta wallafa.
A bayyane yake, ma'auratan sun fara haduwa ne bayan babban dan angon ya hada musu wata ganawa. Hakan ne tushen wannan soyayyar wacce ta kai ga aure.
KU KARANTA: Bidiyon 'yar majalisa matar aure ɗare-ɗare a cinyar dan majalisa ya janyo cece-kuce
Matar mai suna Bose ta rubuta: "Ni bazawara ce kuma ina cikin shekaruna na 50 yayin da Patrick ke cikin shekarunsa na sittin.
"Muna da yara manya 7 da jikoki 4. Babban dan sa ne ya hada mana wani cin abincin dare a Ingila wanda daga nan muka kulle.
"Labarin soyayyarmu yana cike da mamaki. A yanzu mun kasance mata da miji duk da shekarunmu."
KU KARANTA: Nasara daga Allah: Bidiyon sojin sama suna ragargaza shugabannin Boko Haram
A wani labari na daban, wani matashi dan Najeriya ya bar jama'a a kafar sada zumuntar zamani cike da mamaki bayan ya bada labarin rabuwarsa da tsohuwar budurwarsa.
Ya ce ta bashi na'ura mai kwakwalwa kyauta a ranar zagayowar haihuwarsa domin ya fara damfara a yanar gizo.
Kamar yadda ya bayyana a labarin, ta ce bata jin dadin albashinsa domin baya isarsu. Don haka ta bashi kyautar ne don ya shiga gungun wasu masu damfarar yanar gizo.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng