Buhari da Osinbajo zasu karbi allurar rigakafin korona, za'a nuna a talabijin kowa ya gani

Buhari da Osinbajo zasu karbi allurar rigakafin korona, za'a nuna a talabijin kowa ya gani

- Shugabanni da manyan jagororin al'umma na cigaba da karbar allurar rigakafin kwayar cutar korona

- A ranar Alhamis ne tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abunakar, ya karbi allurar rigakafin a kasar Dubai

- A yayin da ake sa ran Nigeria za ta samu rigakafin a karshen wata, NPHC ta ce za'a fara yi wa Buhari da Osinbajo kuma a nuna kai tsaye a gidan TV

Babban daraktan hukumar kiwon lafiya a matakin farko (NPHC), Faisal Shu'aibu, ya ce za'a fara yi wa shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, da mataimakinsa, Yemi Osinbajo, allurar riga-kafin cutar COVID-19 kai tsaye ta akwatin talabijin.

Kimanin kwayar maganin riga-kafin cutar ta COVID-19 100,000 ake sa ran shigo da su ƙasar nan a ƙarshen watan Janairu, kamar yadda TheCable ta rawaito.

Da ya ke ganawa da kwamiti na musamman kan yaƙi da yaɗuwar cutar korona a Abuja, Shu'aibu ya ce za'a nuna yin riga-kafin kai tsaye ta kafar talebijin a ƙoƙarin wayar da kan jama'a domin su rungumi rigakafin.

KARANTA: Bai kamata ya kara ko kwana daya akan mulki ba; Trump ya na kan siradin tsigewa

Ya ƙara da cewa, zakakuran ma'aikatan lafiya za su mayar da hankali wajen karɓar allurar rigakafin da zarar ta iso ƙasar.

Buhari da Osinbajo zasu karbi allurar rigakafin korona, za'a nuna a talabijin kowa ya gani
Buhari da Osinbajo zasu karbi allurar rigakafin korona, za'a nuna a talabijin kowa ya gani @PresidencyNGR
Source: Twitter

"Za mu so ganin manyan shugabanni kamar shugaban ƙasa, mataimakinsa, da shugaban ma'aikata su zo su karɓi allurar a bainar jama'a domin tabbatar musu da cewa riga-kafin ba ya cutarwa. Don haka dole mu shiryawa hakan," a cewarsa.

KARANTA: Bidiyon tsohon shugaba Obasanjo ya na motsa jiki ta hanyar tikar rawa da jama'a

Ya ci gaba da cewa "Ko da a ƙasashen da suka ci gaba, mun ga yadda bayan bawa ma'aikatan lafiya fifiko, shugabanni ma akan fifita su idan ba so ake cutar ta harbesu ba."

Ya kara bada misalin cewa: "Misali ko a wajen yaƙi, idan kana son kashe abokin gaba sai ka nemi muhimman shugabanninsu, da zarar ka gama da su, sauran sojojin ma za su rasa kwarin gwiwa.

Da safiyar ranar Alhamis ne Legit.ng ta rawaito cewa tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya karbi allurar rigakafin cutar COVID-19 a kasar Dubai.

Ana ganin cewa shine sanannen dan Najeriya na farko da ya karbi allurar rigakafin kwayar cutar korona tun bayan fitowarta.

The Cable ta ruwaito cewa mai magana da yawun Atiku, Paul Ibe, shine ya bayyana hakan ranar Alhamis.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Online view pixel