Da ɗuminsa: Gobara ta tashi a hedkwatar hukumar Kula da Shige da Fice ta Ƙasa

Da ɗuminsa: Gobara ta tashi a hedkwatar hukumar Kula da Shige da Fice ta Ƙasa

- Gobara ta lashe wasu ofisoshi a hukumar hedkwatar hukumar NIS da ke Abuja

- Jami'an hukumar kashe gobara na tarayya da taimakon wasu hukumomi sun kashe wutan

- Hukumar da ke Kula da Shige da Fice na ƙasa ta ce gobarar ba zai shafi ayyukan ta ba

Hedkwatar hukumar Kula da Shige da Fice na Ƙasa, (NIS) da ke Abuja ta yi gobara a ranar Lahadi.

Hukumar ta sanar da hakan ne ta shafinta na Twitter inda ta ce wutan ya lalata wasu ofisoshi da ke hedkwatar hukumar.

Da ɗuminsa: Gobara ta tashi a hedkwatar hukumar Kula da Shige da Fice ta Ƙasa
Da ɗuminsa: Gobara ta tashi a hedkwatar hukumar Kula da Shige da Fice ta Ƙasa. Hoto: @MobilePunch
Asali: UGC

DUBA WANNAN: Wani dan shekara 83 zai yi wuff da yarinya mai shekaru 16

Ma'aikatan kwana kwana sun yi nasarar kashe gobarar da a yanzu ba a san dalilin ta ba.

NIS ta ce, "An yi gobara a Hedkwatar mu da safiyar yau. Ya shafi wasu daga cikin ofisoshin mu.

"Jami'an hukumar kashe gobara ta tarayya da taimakon wasu hukumomi kusa da filin tashin jirgin sama sun kashe wutar.

KU KARANTA: Hanan Buhari tare da mijinta Turad sun tafi Dubai don bikin zagayowar ranar haihuwarsa (Bidiyo da Hotuna)

"Ba a san abinda ya yi sanadin gobarar ba amma ana bincike. Muna tabbatar wa al'umma cewa gobarar ba zai shafi ayyukan mu ba."

A wani labarin daban, rikici ya kaure a zauren majalisar Jihar kasar Ghana a jiya Laraba 6 ga watan Janairu bayan rushe majalisar kunshi ta bakwai.

A cikin hoton bidiyon da ya karade shafukan dandalin sada zumunta, an gano rikici ne ya kaure tsakanin yan jam'iyyar NPP da NDC kan wacce jam'iyya ne ke da rinjaye kuma wacce zata fitar da sabon Kakakin Majalisa.

Kamar yadda bidiyon ya nuna, wasu daga cikin yan majalisar sun rika kai wa juna hannu sannan wasu suka rika fatali da akwatunan kada kuri'a da ke zauren majalisar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164