Kwana 3 jere, sama da sabbin mutane 1500 suka kamu da Koronan kullum

Kwana 3 jere, sama da sabbin mutane 1500 suka kamu da Koronan kullum

- Adadin masu kamuwa da Korona yana karuwa kullum tun da aka shiga sabuwar shekara

- Kwanaki uku a jere, yan Najeriya sama da 1500 ke kamuwa da Korona

- Gwamnatin tarayya ta yi barazanar sake kafa dokar hana fita

Mutane 1544 kwayar cutar ta harba a fadin Nigeria a ranar Juma'a, 8 ga watan Junairu 2021, kamar yadda alkaluman hukumar hana yaduwar cututtuka NCDC ta saba fitarwa kullum.

Adadin da aka samu ranar Alhamis ya kai jimillan wadanda suka kamu da cutar 97,478 a Najeriya.

Daga cikin mutane kimanin 98,000 da suka kamu, an sallami 78,552 yayinda 1342 suka rigamu gidan gaskiya.

Daga cikin wadanda aka sallama ranar Juma'a, akwai mutane 264 da sukayi jinya a gidajensu a jihar Legas, mutane 147 a jihar Plateau, bisa ka'idar hukuma.

Amma an yi rashin mutane 12.

KU KARANTA: Zamu kawo karshen Boko Haram da yan bindiga shekarar nan, shugaba Buhari

KU KARANTA: Sama da mutane 1500 sun kamu cutar Coronavirus ranar Alhamis

Gwamnatin tarayya a ranar Alhamis ya bayyana cewa gaskiya idan adadin sabbin masu kamuwa da cutar Korona ya cigaba da yawa kamar yadda ake samu yanzu, za'a sake kafa dokar hana fita.

Babban jagoran kwamitin yaki da cutar Korona, Dakta Sani Aliyu, ya bayyana hakan yayin hira da manema labarai a Abuja, Punch ta ruwaito.

Aliyu yace, "Idan wannan adadin ya cigaba da yawa haka kuma adadin masu mutuwa ya karu, gaskiya babu wata mafita (illa kulle). Idan bamu son a garkame mu, yanzu ne lokacin da ya kamata mubi dokoki."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng