Kotu ta tsinke aure bayan miji ya yi yunkurin amfani da mata wurin tsafi
- Wata kotu ta raba auren shekara 15 dake tsakanin Fatima da Azeez saboda rashin yardar dake tsakanin ma'auratan
- Fatima tayi zargin mijinta yana yunkurin amfani da dan kamfanta wurin neman kudi ta hanyar tsafi
- Shi kuwa Azeez ya musanta hakan, inda yace kyama ce ta kama shi lokacin da ya ga ta jika kamfan, sai ya jefar a daji
Wata kotu dake jihar Ibadan ta raba auren shekaru 15 dake tsakanin wata 'yar kasuwa, Fatima Akinpelu da Azeez, akan yunkurin amfani da matarsa don tsaface-tsafacen neman kudi.
Yayin da alkalin kotun, Chief Ademola Odunade yake yanke hukunci, ya ce babu dalilin da zai sa Akinpelu da Azeez su cigaba da rayuwar aure, saboda hakan zai iya cutar dasu.
Kotu ta bai wa Akinpelu damar rike dansu mai shekaru 14, yayin da ta umarci Azeez da ya dinga biyanta N5,000 duk wata na ciyarwa, Daily Trust ta ruwaito.
KU KARANTA: Kutse a majalisa: Rayuka 4 sun salwanta, an damke magoya bayan Trump masu yawa
Alkalin ya umarci Azeez da ya yi kokarin bayar da muhimmanci ga ilimin yaron da kuma sauran harkokin rayuwarsa.
Dama Akinpelu ta sanar da kotu yadda tayi korafi akan mijinta, don tana matukar tsoransa.
Kamar yadda ta ce, "Ina tsoron miji na da abinda zai iya aikatawa, don na jika dan kamfai na a bokiti amma sai naga yayi layar zana. Kuma Azeez ne kadai zai iya zuwa inda kamfaina yake.
"Mai girma mai shari'a, da na tambaye shi sai yace ya jefar da shi a daji. Sai dai da na tsananta bincike sai na gane cewa ya wanke jinin dake kamfan kuma ya jefar dashi. Sannan mutum ne wanda bai damu da dansa ba."
Azeez ya musanta zargin da aka yi masa, inda ya ce shi mutum ne mai tsoron Allah, kuma babu abinda zai amfana dashi idan ya cutar da Fatima.
Ya ce Fatima ba matar da za a yarda da ita bace don tana da boye-boye.
Kamar yadda yace, "Yayin da naga ta jika dan kamfan, kyama ta kama ni, sai na watsar da shi a wani daji kusa damu don ina son amfani da bokitin."
KU KARANTA: Hukumar Hisbah ta cafke matasa 53 a kan laifin aikata al'amuran rashin da'a
A wani labari na daban, a wata takarda da kakakin hukumar 'yan sanda, Gambo Isah ya saki, ya tabbatar da yadda 'yan sanda suka kashe 'yan bindiga 6 a jihar Katsina.
'Yan sandan sun kai samame ne a ranar 1 ga watan Janairun 2021, inda suka samu nasarar kwatar miyagun makamai kamar bindigogi kirar G3, AK 47, LAR, bindigogin toka guda biyu da 10 rounds na 7.62mm ammunition a hannunsu.
"A ranar 2/1/2021 sun samu nasarar kwatar AK 47 da 32 rounds na 7.62mm ammunition a Pauwa Bushland dake karamar hukumar Kankara dake jihar Katsina," a cewarsa.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng