Sarkin Iblisai: Mutumin da ya aura mata 57 a jihar Enugu

Sarkin Iblisai: Mutumin da ya aura mata 57 a jihar Enugu

- Wani sanannen mai maganin gargajiya na jihar Enugu, mai suna Simon Odo Alias Onuwa, yana cin karensa babu babbaka

- Yana kiran kansa da sarkin shaidanu, kuma ya auri mata 57 daga kabilu daban-daban, kuma yana shirin kara auren wata ta 58

- Ya bayyana yadda yake da yara fiye da 300, jikoki fiye da 200, kuma duk suke cin abinci daga tukunya daya ba tare da ya gaza ba

Wani mai maganin gargajiya, Simon Odo, wanda aka fi sani da Sarkin shaidanu yana kallon duniya a tafin hannunsa.

Mutumin mazaunin anguwar Aji ne, da ke karamar hukumar Igbo-Eze ta arewa dake jihar Enugu, ya kafa tarihin auren fiye da mata 50 a duniya.

Mutumin mai shekaru 72 da haihuwa ya ce har yanzu bai gama aure ba, duk da matansa 57, giyar duniya tana juyi dashi, don yanzu haka yana shirye-shiryen auren matarsa ta 58.

KU KARANTA: Fitattun mutane10 da rasuwarsu ta matukar girgiza jihar Katsina a 2020

Sarkin Iblisai: Mutumin da ya aura mata 57 a jihar Enugu
Sarkin Iblisai: Mutumin da ya aura mata 57 a jihar Enugu. Hoto daga Sunnewsonline.com
Asali: UGC

Yayin da ake tattaunawa dashi a garinsu, inda mutanen kasar nan da na ketare suke zuwa neman magunguna a wurinsa.

Ya bayyana yadda shi da iyalinsa suke da damar kayar da duk wani dan takara ko kuma su zabe shi saboda tsabar yawansu.

Kamar yadda yace, yana da fiye da jikoki 200, yaransa kuwa sun fi 300, matansa dama 57 ne.

Ya bayyana yadda a baya yake bin addinin kirista yadda ya dace a 1956, daga nan cuta ta same shi a 1960 har sai da ya zama gurgu na tsawon shekaru 5, bayan nan ne aka kai shi Ijebu-Ode, jihar Oyo lokacin kafafunsa sun rube.

Bayan warkewarsa ne ya fara koyon bayar da magunguna wurin wata tsohuwa na tsawon shekaru 2, duk da dai iyayensa basu so hakan ba.

Ya fara aure yana da shekaru 20 a duniya, lokacin yana Ijebu-Ode, yace yana auren mata akalla 3 ko 4 daga ko wacce kabila ko kuma gari, kuma ya ce bai taba amfani da asiri ba kafin ya samu su aure shi.

Onuwa yace kaf matansa masu ilimi ne kuma suna da akalla digiri ko NCE, kuma suna koyarwa.

Yace a tukunya daya ake girkin gidansa. Ba a raba masa abinci kuma ana girki mai rai da motsi.

KU KARANTA: Hukuncin kuskure: Za a biya wani mutum N3.7bn bayan kwashe shekaru 28 a gidan kurkuku

A wani labari na daban, hukumar Hisbah ta jihar Kano ta damke wasu matasa a kan zarginsu da take da hannu cikin al'amuran rashin da'a a birnin Kano, Premium Times ta wallafa.

Kakakin hukumar Hisbah na jihar Kano, Lawal Ibrahim, wanda ya bayyana hakan a ranar Laraba a Kano ya ce an kama su ne sakamakon wani samame da aka kai.

Kamar yadda yace, an kama wadanda ake zargin a daren Talata a lamido Crescent da ke karamar hukumar Nasarawa ta jihar Kano a kan siyar da miyagun kwayoyi.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng

Tags: