Gwamna Zulum ya fara biyan karancin albashi N30,000 a Borno – Kungiyar kwadago ta tabbatar

Gwamna Zulum ya fara biyan karancin albashi N30,000 a Borno – Kungiyar kwadago ta tabbatar

Kungiyar kwadago ta Najeriya a ranar Juma’a, 24 ga watan Janairu ta tabbatar da cewar mafi akasarin ma’aikatan Borno sun amshi albashinsu na watan Janairu 2020 da karin karancin albashi na 30,000 da Gwamna Babagana Zulum Umara ya aiwatar.

Shugaban kungiyar kwadago a jihar Borno, Kwamrad Bulama Abiso ne ya tabbatar da hakan a wani wasika zuwa a tawagar labarai na gwamnan a safiyar ranar Juma’a don watsawa.

“Gwamnatin jihar Borno karkashin jagorancin Farfesa Babagana Umara Zulum ta fara aiwatar da sabon karancin albashi 30,000 ga ma’aikata.

“Kungiyar kwadago a jihar Borno ta yaba ma gwamnan kan cika alkawarinsa na daukar jindadin ma’aikata da muhimmanci. Muna kira ga ma’aikatan gwamnati da su biya wannan karamcin ta hanyar sake jajircewa kan aiki” in ji shugaban kwadagon.

Abiso ya bayar da tabbacin cewa koda dai kungiyar bata samu kowani korafi ba tukuna, a shirye take ta kokawa gwamnati idan wani ma’aikaci ya gaza ganin kari a albashin Janairu.

KU KARANTA KUMA: Gwamnatin Buhari ta kashe naira Tiriliyan 1.7 kan wutan lantarki da yake a durkushe – El-Rufai

Sannan kungiyar kwadagon ta roki gwamna Zulum da ya isar da karin albashin har zuwa kananan hukumomi da mahukuntan makarantun kananan hukumomi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel