Buhari ya maye gurbin Ishaq Bello da Salisu Garba a babbar kotu Abujan

Buhari ya maye gurbin Ishaq Bello da Salisu Garba a babbar kotu Abujan

- A ranar Laraba, 06 ga watan Janairu, ne mai shari'a Ishaq Bello, babban alkalin kotun Abuja, ya yi murabus

- Sakamakon ritayarsa ne shugaba Buhari ya amince da nadin Salisu Garba a matsayin madadinsa

Sakamakon ritayar babban jojin ƙasar nan, mai Shari'a Ishaq Bello, shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, ya baiwa Salisu Garba, muƙamin riƙon babban joji a babbar kotun kasa da ke Abuja, kamar yadda TheCable ta rawaito.

A wata takarda wacce daraktan sadarwa a ma'aikatar Shari'a na ƙasa ya fitar, ya ce alkalin alkalai na kasa (CJN), Mai Shari'a Ibrahim Muhammad, ne zai rantsar da Garba ranar Larabar nan.

"Sakamakon ritaya da mai girma Ishaq Bello ya yi a yau (Laraba), shugaba Muhammadu Buhari, GCFR, ya sahale da naɗin mai girma Salisu Garba a matsayin mai riƙo."

"In Allah ya kai mu gobe ne (Laraba), mai girma mai Shari'a I.T Muhammad, CFR, zai rantsar da shi da misalin ƙarfe 2:00 na rana," kamar yadda sanarwa ta bayyana.

KARANTA: Da gyara a jawabinka na sabuwar shekara; Dattijan arewa sun aika sako ga Buhari

Sabon alkalin da Buhari ya amince da nadinsa dan asalin karamar hukumar Malumfashi ta jihar Katsina ne.

Buhari ya maye gurbin Ishaq Bello da Salisu Garba a babbar kotu Abujan
Buhari ya maye gurbin Ishaq Bello da Salisu Garba a babbar kotu Abujan
Asali: UGC

KARANTA: Ina kisa ne domin kawai na samu kudin shan giya da shagwaba budurwata - Matashi Tajudeen

Salisu Garba ya samu zama cikakken lauya a 1984 ya kuma kammala bautar ƙasa a shekarar 1985.

A baiwa Garba muƙamin majistare a babbar kotu a 1989. A 1997 ya sama babban rijistara a babbar kotun tarayya ya zama alkalin babbar kotun tarayya a 1998.

A wani labarin, Legit.ng Hausa rawaito cewa Sakamakon ƙalubalen hare-hare na Boko Haram, ƙasashen Yamma sun fi nuna damuwa da jihar Borno sama da ƙasashen Larabawa waɗanda suma suke fama da irin wannan matsalar, kamar yadda Vanguard ta rawaito.

Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ne ya bayyana hakan ranar Talata yayin da yake karɓar baƙuncin ambasadan Falasɗinawa, Saleh Fheised Saleh, inda ya jinjinawa yankin na Falasɗinu da zama ɗaya tamkar da dubu a yankin gabas ta tsakiya.

A cewar gwamnan, babu wata kasar Larabawa a baya da ta bawa Jihar Borno tallafin da kasashen Turai suka bayar.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel