Kabilar Yarabawa: Camfi da al'adu 9 da baka taba jin labarinsu ba

Kabilar Yarabawa: Camfi da al'adu 9 da baka taba jin labarinsu ba

- Kowacce kabila tana da wasu camfi ko kuma a ce wasu al'adu da suka yadda da su

- Kabilar Yarabawa tana daya daga cikin manyan kabilun da ke da jama'a masu yawa a kasar nan

- Daga cikin camfin akwai rashin shan ruwan kwakwa, yawo da allurai a jikin rigar mace mai juna biyu

Daga dalilin da zai sa mata mai juna biyu ta dinga manne kayanta da allurai zuwa ga dalilin da zai hana shan ruwan kwakwa, akwai wasu camfi masu bada mamaki kuma ba dole mai karatu ya taba jinsu ba a al'adar Yarabawa.

Kabilar Yarabawa tana daya daga cikin manyan kabilun da ke kasar nan kuma suna da mutane masu tarin yawa.

Kamar kowacce kabila dai, an san wannan kabilar da riko da al'adunta tare da addini. Daga cikin al'adun ne akwai wasu masu bada mamaki wadanda kuma kai tsaye za a iya ce musu camfi.

Ga wasu daga cikin camfi tare da al'adu 9 na kabilar da ba dole mai karatu ya taba jinsu ba.

1. Mace mai juna biyu dole ne ta manne kayanta da allurai.

A yadda jama'ar kabilar nan suka yadda, ba daidai bane mace mai juna biyu ta bar kayan jikinta babu allurai. Hakan kai tsaye gayyatar miyagun aljanu ne ga dan da ke cikinta.

2. Babban abun ashsha ne wasa da lema yayin da ba a ruwan sama

Duk wanda ke wasa da lema ba a ruwan sama yana gayyatar ruwan sama mai matukar yawa ne a ranar aurensa.

KU KARANTA: BUK ta soke zangon karatu na 2019/2020, ta sanar da ranar komawar dalibai

Kabilar Yarabawa: Camfi da al'adu 10 da baka taba jin labarinsu ba
Kabilar Yarabawa: Camfi da al'adu 10 da baka taba jin labarinsu ba. Hoto daga Pulse.ng
Source: UGC

3. Ba a tsuwwa cikin dare

Duk mai tsuwwa cikin dare kai tsaye yake kiran macizai da danginsa zuwa gidansa.

4. Mace mai juna biyu bata yawo a rana

A wannan kabilar, an sakankance cewa duk idan mace mai juna biyu tana yawo da tsakar rana toh tabbas za ta haifa nakasasshen jinjiri. A don haka ake hana mace mai juna biyu yawo a rana.

5. Ba a dukan yaro namiji da tsintsiya

Dukan yaro namiji da tsintsiya kamar yadda Yarabawa suka camfata yana hana su haihuwa.

6. Ba a shan ruwan kwakwa

Kamar yadda suka yadda, a duk lokacin da mutum ya sha ruwan kwakwa, toh tabbas zai zama dakiki.

7. Ba a kallon madubi da dare

Kamar yadda suka yarda, ba a kallon madubi da dare saboda a maimakon ganin mutum, sai a ga aljani.

8. Silin zare daya zai iya tsayar da shakuwa

Wannan ana yin shi ne ga jarirai kamar yadda suka yadda. A duk lokacin da jariri ya fara shakuwa ana saka mishi zare a kan shi domin ta tsaya.

9. Ba a tsallake mutum

Idan mutum ya tsallakw ka, za ka haifa da mai kama da shi sai dai idan ya dawo ya sake tsallakawa.

KU KARANTA: Hotunan ziyarar da Zulum ya kai wa mafarautan da Boko Haram suka kaiwa hari

A wani labari na daban, fusatattun matasa a jihar Katsina a jiya sun fito zanga-zanga tare da rufe manyan tituna sakamakon fusata da garkuwa da mutane tare da harin 'yan bindiga a kauyukansu.

Matasan da suka fito daga kauyuka daban-daban na karamar hukumar Dandume sun rufe babban titin da ke hada yankin da karamar hukumar Funtua ta jihar.

A ranar lahadi jaridar Daily Trust ta gano cewa matasan sun mamaye titin inda suka yi barazana ga gwamnati a kan ta dauka mataki ko kuma su samo hanyar kare kansu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Online view pixel