Basarake ya zargi ƴan sandan Legas da azabtar da ɗansa har sai da ya mutu

Basarake ya zargi ƴan sandan Legas da azabtar da ɗansa har sai da ya mutu

- Basaraken Abule-Okuta a Legas yana zargin yan sanda da kashe ɗansa Taiwo

- Ya ce wani matashi ne ya yi ƙarar ɗansa ofishin yan sanda bayan sun samu saɓanin

- Daga nan kuma ƴan sandan suka kama ɗansa suka kai shi caji ofis suka azabtar da shi

Basaraken garin Abule-Okuta, Bariga a Legas, Wasiu Jinadu, ya yi zargin cewa ƴan sandan Bariga da azabtar da ɗansa, Taiwo, har sai da ya mutu.

Punch Metro ta gano cewa an kama Taiwo ne a ranar Kirsimeti bayan wani ɗan kwallo, Toyin, ya yi kararsa wurin ƴan sanda cewa ya naushe shi sakamakon rashin jituwa da suka samu.

Jinadu ya shaidawa majiyar Legit.ng cewa ƴan sandan sun garzaya da ɗansa asibiti bayan azabtar da shi inda ya mutu.

Basarake ya zargi ƴan sandan Legas da azabtar da ɗansa har sai da ya mutu
Basarake ya zargi ƴan sandan Legas da azabtar da ɗansa har sai da ya mutu. Hoto daga @MobilePunch
Source: Twitter

KU KARANTA: 'Yan Boko Haram sun kai farmaki sansanin sojoji, sun kashe 7, sun raunata wasu

Ya ce, "A ranar Juma'a, 25 ga watan Disamba, ɗa na da abokansa suna shagalin Kirsimeti a Alubarika Street a Bariga sai wani Toyin da suka samu saɓani ya yi ƙararsa wurin yan sanda cewa Taiwo ya naushe shi a baki.

"Ɗa na ya tafi kasuwa siyan kaya yana hanyar dawowa sai ƴan sanda garin ƙoƙarin kama shi suka tura shi da babur ɗinsa cikin kwata kafin suka tafi da shi ofishin su.

"Abokan Taiwo sun faɗa min abinda ya faru, an bani tabbacin babu matsala. Amma kwatsam, Toyin ya zo wuri na karfe 5 na asuba ya haɗu da ƙanin Taiwo, Gbolahan.

"Ya fadawa Gbolahan cewa 'yan sanda sun ce Taiwo ba shi da lafiya don haka sun kai shi asibiti. Gbolahan da Toyin sun tafi asibiti don duba shi amma da suka isa sai suka samu wani abu mai kumfa na fitowa daga bakin Taiwo."

Basaraken ya ce ma'aikaciyar jinya ta faɗa masa cewa yan sandan sun ce Taiwo ya faɗa kwata saboda yana cikin maye.

KU KARANTA: Akwai ƙyakyawar alaƙa tsakani na da Ganduje da Kwankwaso, in ji Shekarau

Daga bisani dai Taiwo ya rasu bayan an yi ƙoƙarin ceto ransa a asibitin LASUTH.

Kakakin ƴan sandan Jihar, Muyiwa Adejobi ya tabbatar da cewa ƴan sanda sun kama marigayin.

Sai dai ƴan sandan sun musanta cewa azabtar da Taiwo aka yi har ya mutu, "Ya samu rauni ne saboda ya daka tsalle daga motar yan sanda domin yana cikin maye."

A wani labari na daban, hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta Jihar Kano (PCACC) ta bankado ayyukan almundahana a tallafin karatun kasashen waje na gwamnatin jihar, Daily Trust ta ruwaito.

Shugaban hukumar, Magaji Rimingado, wanda ya bayyana haka ga yan jarida ranar Talata, ya ce daga 2015 zuwa 4 ga Janairun 2021, gwamnatin jihar ta kashe naira biliyan 7 a tsarin wanda ta gada daga gwamnatin da ta gabata, amma ana samun korafin daliban da suka rage a kasashen waje.

Ganin yadda korafe korafe suka yi yawa kuma ya kamata ace da yawa yawancin daliban sun kammala karatun su, gwamnan jihar, Abdullahi Umar Ganduje ya umarci hukumar da tayi "bibiya", bincika ta kuma dauki mataki akan badakalar", in ji Rimingado.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel