Bidiyon budurwa gurfane tana kuka a gaban saurayi a titi ya janyo cece-kuce

Bidiyon budurwa gurfane tana kuka a gaban saurayi a titi ya janyo cece-kuce

- Wani bidiyon mace da namiji suna wata tattaunawa maras dadi yayin da matar ke rike rigar namijin ta bazu a kafar sada zumunta

- A cikin dakika kalilan, budurwar ta fara kuka yayin da ta gurfana guiwarta bibbiyu tana rokon mutumin da ake zargin saurayinta ne

- 'Yan kasar Kenya da ke Twitter sun dora laifin wannan lamari a kan saurayin yayin da wasu suka ce budurwar bata da aji

A wani bidiyo da ya karade kafafen sada zumuntar zamani na Twitter, an ga wata budurwa a Nairobi ta gurfana guiwa bibbiyu a titi a gaban saurayi, lamarin da ya janyo cece-kuce.

A yayin da aka fara nadar bidiyon, an ga budurwa da saurayin suna wata tattaunawa wacce babu shakka bata da dadi.

Babu jmawa kuwa aka ga budurwa ta zube kasa guiwa bibbiyu a titin tana jnayo rigar saurayin, alamun bada hakuri.

KU KARANTA: Ba zan taba yafe mata ba, Matar aure da kishiya ta babbaka da ruwan zafi

Bidiyon budurwa gurfane tana kuka a gaban saurayi a titi ya janyo cece-kuce
Bidiyon budurwa gurfane tana kuka a gaban saurayi a titi ya janyo cece-kuce. Hoto daga @Shobanes
Asali: Twitter

A yayin da saurayin ya ga hankalin jama'a ya koma kansu gaba daya, ya yi kokarin kubucewa amma ya kasa saboda tsananin rikon da budurwar tayi masa.

Ayayin da masu kallo daga nesa suka fara matsowa kusa domin ganin me ke faruwa, hakan bai sa budurwar ta ji kunya ba. Ta cigaba da rokon saurayin wanda a bayyane yake harzuke.

Anji mutane na cewa, "Rabuwa zai yi da ita shine ta ki amincewa," amma da yarensu.

Babu shakka wanan bidiyon ya janyo cece-kuce a kafar sada zumuntar zamanin. Ga bidiyon tare da tsokacin jama'a:

KU KARANTA: Hotunan ziyarar da Zulum ya kai wa mafarautan da Boko Haram suka kaiwa hari

A wani labari na daban, wata kyakkyawar lauya mai daukaka tayi wata wallafa a shafinta na kafar sada zumuntar zamani ta Twitter wacce ta janyo cece-kuce.

Budurwar mai suna Barrister Khadijah Umar, mai amfani da suna @Barrkhadijah, ta ce rayuwa babu miji bata da dadi, komai nasarar da mace ta samu a rayuwa.

Wannan wallafar ta ta ci karo da ta wasu mata wadanda suke nuna cewa macen da take samun fiye da N500,000 duk wata, bata bukatar namiji a rayuwarta.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel