COVID-19: NCDC ta sanar da kamuwar sabbin mutum 1354
- Najeriya a ranar Talata, 5 ga watan Janairu, ta sake samun sabbin mutanen da suka kamu da annobar korona
- Hukumar NCDC ta sanar da cewa sabbin mutane 1,354 ne suka harbu da annobar a jihohi 22 inda Lagas ke kan gaba a wannan karon ma
- An kuma samu karin mutum daya da ya mutu yayinda jimilar wadanda suka kamu ya kai 92,705 inda 76,396 suka warke
Hukumar da ke yaki da hana yaduwar cututtuka a Najeriya (NCDC) ta sanar da samun karin mutane 1,354 da suka harbu da annobar korona a ranar Talata, 5 ga watan Janairu.
An samu sabbin wadanda suka kamu ne a jihohi 22 inda Lagas wacce ta kasance cibiyar annobar a Najeriya ke kan gaba a yawan mutanen da suka kamu da cutar cikin kwana daya da mutum 712.
Sai kuma babbar birnin tarayya da ke bi mata inda ta samu karin mutum 145 da suka harbu yayinda Plateau, Kwara da Kaduna suka biyo baya da 117, 81 da 54 kowannensu.
Jihar Sokoto na da 39, Oyo na da 38, Rivers 37 sannan Gombe na da 21. Enugu da Akwa Ibom suka biyo baya da 20 da 16 kowannensu.
KU KARANTA KUMA: Gwamnan PDP ya jinjinawa shirin gwamnatin tarayya na daukar ayyuka na musamman
Jihohin Bauchi da Delta na da mutum 14 kowanne, sai Ebonyi mai 13. Anambra kuma na da mutum 9, Taraba 8 sannan Edo ma 8.
Kano na da karin mutum 3, Osun na da 2, Ekiti ma na da 2 yayinda jihar Ogun ta zo karshe da mutum daya.
KU KARANTA KUMA: PDP ta ce babu wani gwamnan kudu maso gabas a karkashin inuwarta da ke shirin sauya sheka
Da wannan kididdiga, yawan mutanen da suka harbu da cutar korona a Najeriya sun kai 92,705.
Zuwa yanzu an sallami mutane 76,396 daga asibiti bayan sun warke daga cutar sannan mutane 1,319 ne suka mutu tun bayan bullar cutar a kasar a watan Fabrairun 20202.
A wani labarin, wani uban yara biyar ya tsere bayan matarsa ta haifi yara hudu zur a ranar Asabar, 2 ga watan Janairu a Benin, babbar birnin jihar Edo.
Wata mai amfani da shafin Facebook mai suna Sarah Az Izevbigi ce ta bayyana hakan. A cewar matar, mai jegon mai suna Rita Ndibisu, na bukatar taimakon yan Najeriya don kula da yaranta.
Ta roki yan Najeriya da su taimaki Rita da yaranta yayinda ta wallafa asusun bankin da za a sa kudin.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng