Kyakyawar budurwa lauya ta ce ta gaji da zama babu miji, tana bukatar wanda za su ci dukiyarta tare (Hotuna)
- Wata kyakkyawar lauya mai suna Barrkhadija, ta yi wata wallafa a Twitter wacce ta janyo cece-kuce
- A cewarta, duk da ta samu daukaka mai tarin yawa amma rayuwa bata mata dadi tunda bata da miji
- Kamar yadda lauyar tace, tana bukatar namijin da za ta dinga kashe dukiyarta tare da shi
Wata kyakkyawar lauya mai daukaka tayi wata wallafa a shafinta na kafar sada zumuntar zamani ta Twitter wacce ta janyo cece-kuce.
Budurwar mai suna Barrister Khadijah Umar, mai amfani da suna @Barrkhadijah, ta ce rayuwa babu miji bata da dadi, komai nasarar da mace ta samu a rayuwa.
Wannan wallafar ta ta ci karo da ta wasu mata wadanda suke nuna cewa macen da take samun fiye da N500,000 duk wata, bata bukatar namiji a rayuwarta.
Kyakkyawar lauyar ta nuna cewa kudi ba matsalarta bace, namiji ne kadai matsalarta. Kamar yadda ta wallafa, "Ina bukatar namijin da zamu dinga cin kudina tare da shi.
KU KARANTA: Hotunan ziyarar da Zulum ya kai wa mafarautan da Boko Haram suka kaiwa hari
Wannan wallafar ta janyo cece-kuce iri-iri inda wani abba_dra cewa yayi: "Eh! Kuma duk wani namiji mai hankali, dukiya, ilimi, nasara da daukaka, akwai wata mace wacce ta tsaya masa. Dole mutum ya dogara da wani."
Mubaraksaba1 ya ce: "Haka rayuwa take 'yar uwa, yau da gobe sai Allah. Allah ya taimakemu."
Wata UmeorizuP ta ce: "Mu din dai muke korafin cewa bamu bukatar namiji, yanzu kuma mun samu daukaka muna bukatar namiji. Toh, ga dai mu nan."
KU KARANTA: Yanzu-yanzu: Allah ya yi wa Iyan Zazzau, Alhaji Bashir Aminu rasuwa
A wani labari na daban, Gwamnatin tarayya ta gurfanar da Omoyele Sowore da wasu mutane hudu a gaban wata kotun majistare da ke Wuse Zone 2, Abuja, jaridar Leadership ta wallafa.
Rundunar 'yan sandan Najeriya ce ta gurfanar da Sowore a kan jagorantar zanga-zangar da suka yi wa gwamnati a ranar 31 ga watan Disamban 2020 a Abuja.
An gurfanar da shi tare da wasu mutane hudu a kan zarginsu da ake da lafifuka uku, lamarin da suka musanta aikatawa.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng