BUK ta soke zangon karatu na 2019/2020, ta sanar da ranar komawar dalibai

BUK ta soke zangon karatu na 2019/2020, ta sanar da ranar komawar dalibai

- Hukumar gudanarwa ta BUK ta aminta da soke zangon karatu na 2019/2020 da dalibai suka fara

- Hukumar ta bayyana ranar 18 ga watan Janairun 2020 a matsayin ranar komawar dalibai

- Ta kara da daga kafa ga masu karatun digiri na biyu da na uku wurin biyan kudin makaranta

Hukumar gudanarwa ta jami'ar Bayero da ke Kano ta amince da soke zangon karatu na 2019/2020 da aka fara a dukkan fadin makarantar.

Wannan na kunshe ne a wata takarda da rijistirar makarantar, Fatima Binta-Mohammed ta saka hannu.

Kamar yadda takardar ta bayyana, ga dalibai masu digirin farko, za su fara zangon karatunsu ne a ranar 18 ga watan Janairu yayin da sashi na biyu na zangon karatunsu zai fara a ranar 3 ga watan Mayun 2021.

BUK ta soke zangon karatu na 2019/2020, ta sanar da ranar komawar dalibai
BUK ta soke zangon karatu na 2019/2020, ta sanar da ranar komawar dalibai. Hoto daga @daily_nigerian
Source: Twitter

Ga masu digiri na biyu da na uku, hukumar gudanarwar ta bayyana ranar 18 ga watan Janairu da zama ranar farko ta sashin karatu na farko inda sashi na biyu zai fara a 1 ga watan Yuni.

Har ila yau, hukumar ta amince da daga kafa ga masu digiri na biyu da na uku wadanda basu biya kudin makaranta ba da su gaggauta biya kafin a fara karatu.

Jaridar Daily Nigerian ta gano cewa hukumar gudanarwan ta soke zangon karatun 2019/2020 inda ta maye gurbinsa da na 2020/2021.

Idan za mu tuna, kungiyar malamai masu koyarwa na jami'o'i ta fada yajin aikin sai baba ta gani a ranar 23 ga watan Maris na 2020 kuma ta koma a ranar 22 ga watan Disamba.

KU KARANTA: Ba zan taba yafe mata ba, Matar aure da kishiya ta babbaka da ruwan zafi

BUK ta soke zangon karatu na 2019/2020, ta sanar da ranar komawar dalibai
BUK ta soke zangon karatu na 2019/2020, ta sanar da ranar komawar dalibai. Hoto daga @daily_nigerian
Source: Twitter

KU KARANTA: Hotunan ziyarar da Zulum ya kai wa mafarautan da Boko Haram suka kaiwa hari

A wani labari na daban, Shugaban jam'iyyar APC na gundumar Gwargwada da ke karamar hukumar Toto ta jihar Nasarawa tare da daukacin mabiyansa sun koma jam'iyyar APC a jihar, Daily Trust ta ruwaito.

Shugaban jam'iyyar, Danlami Yanga tare da mabiyansa sun sanar da sauya shekarsu zuwa APC a wani taron masu ruwa da tsaki da aka yi a garin Gadabuke.

Ya ce: "Ni da mabiyana mun yanke hukuncin barin PDP tare da komawa jam'iyyar APC sakamakon salon mulkin Gwamna Abdullahi Sule da kuma kakakin majalisar jiha, Balarabe Abdullahi."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel