Ganduje: Sabuwar alaka da ke tsakanin Shekarau da Kwankwaso ta tada kura a kan gabatowar 2023

Ganduje: Sabuwar alaka da ke tsakanin Shekarau da Kwankwaso ta tada kura a kan gabatowar 2023

- Sanannan lamari ne idan aka ce Sanata Shekarau da Sanata Kwankwaso basu zama inuwa daya a siyasance

- Sun kasance manyan abokan adawan juna, amma hakan bai hana Shekarau zuwa ta'aziyyar mahaifin Kwankwaso ba

- Masu kiyasi da nazarin siyasa a Kano suna ganin sabuwar alakar za ta iya zama wani hange ce a siyasar Kano a 2023

Sanata Ibrahim Shekarau da Sanata Rabiu Musa Kwankwasoo, dukkansu tsofaffin gwamnonin jihar Kano sun kasance tsoffin makiya a siyasance wadanda basu iya zama a inuwa daya ballantana a siyasa.

Shekarau ya kayar da Kwankwaso a 2003 a lokacin da Kwankwaso yake neman zarcewa. Kwankwaso ya yi nasarar a 2011 inda ya kayar da Salihu Sagir Takai a zaben gwamnoni.

Kwankwaso ya sake nasara bayan Ganduje dan takararsa ya maka Takai dan takarar Shekarau da kasa.

KU KARANTA: Ba zan taba yafe mata ba, Matar aure da kishiya ta babbaka da ruwan zafi

Ganduje: Sabuwar alaka da ke tsakanin Shekarau da Kwankwaso ta tada kura a kan gabatowar2023
Ganduje: Sabuwar alaka da ke tsakanin Shekarau da Kwankwaso ta tada kura a kan gabatowar2023. Hoto daga @daily_trust
Source: Twitter

Shekarau ya bar jam'iyyar APC a 2014 bayan da Kwankwaso ya bar PDP ya koma kuma aka bashi ragamar jam'iyyar.

Bayan shekaru hudu, Kwankwaso ya koma PDP kuma an bashi shugabancinta, lamarin da yasa Shekarau ya koma APC.

Wadannan lamurran sun sa masu kiyasin siyasa a Kano sun gano cewa ba abu ne mai sauki ba zaman Kwankwaso da Shekarau a jam'iyyar siyasa daya.

Amma kuma, bayan rasuwar mahaifin Kwankwaso a ranar 25 ga watan Disamba, ta'aziyyar da Shekarau ya je ta janyo cece-kuce daga masu nazarin siyasa inda suke tunanin akwai yuwuwar su dinke barakar sannan su hada kai don kwace ragamar siyasar jihar a 2023.

KU KARANTA: Shugaban PDP da daukacin mabiyansa baki daya sun sauya sheka zuwa APC

A wani labari na daban, kamar yadda BBC Hausa ta yi hira da babban malami, Sheikh Gumi a kan dalilinsa na shiga yankuna masu tsananin hadari domin da'awa, malamin ya bayyana dalilinsa. Malamin ya bayyana dalilansa biyu na yin hakan.

Ya ce: "Wadannan bayin Allah dai makiyaya ne kuma a daji suke zama. Suna matukar bukatar wanda zai koyar musu da addini. Akwai bukatar su fita daga cikin jahilcin da suka tsinci kansu. Bautar Allah ta zama dole."

Malamin ya tabbatar da cewa barnar da suka fada ta samo asali ne da rashin ilimin da suke ciki.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel