Farfesa Zulum: Tsaro ya karu a jihar Borno karkashin shugabancin Buhari

Farfesa Zulum: Tsaro ya karu a jihar Borno karkashin shugabancin Buhari

- Farfesa Babagana Umara Zulum ya ce tsaro ya karu a jihar Borno da arewa ma so gabas a karkashin mulkin Buhari

- A cewar gwamnan, shaidu a kasa sun nuna cewa al'amuran harkokin rayuwa sun fara dawowa a kananan hukumomin da jama'a suka kauracewa a baya

Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya ce duk da kisan manoma 43 da mayakan kungiyar Boko Haram su ka yi a Zabarmari, tsaro ya karu a jihar a karkashin mulkin shugaban kasa, Muhammadu Buhari, kamar yadda Punch ta rawaito.

Farfesa Zulum, ya bayyana hakan ne ranar Lahadi yayin da ya karbi bakuncin kungiyar dattijan arewa a karkashin jagorancin shugabanta, Ambasada Shehu Malami, da kuma sakatarenta, Audu Ogbeh.

Hakan na kunshe ne a cikin jawabin da gwamnatin jihar Borno ta fitar ranar Litinin mai taken 'Zulum: Duk da kashe-kashe, shaidu a kasa sun nuna cewa an fi samun zaman lafiya a karkashin mulkin Buhari a Borno.

KARANTA: Yaba kyauta: Kasar Amurka ta yafewa ƴan Najeriya kuɗin Biza, ta bayar da adireshin shafin yanar gizo

Farfesa Zulum: Tsaro ya karu a jihar Borno karkashin shugabancin Buhari
Farfesa Zulum: Tsaro ya karu a jihar Borno karkashin shugabancin Buhari @Bashirahmad
Asali: Twitter

Jawabin ya rawaito Zulum na cewa, "daga bayanai da mu ka samu daga kananan hukumomi 27 na jihar Borno tun daga shekarar 2011, shaidu sun nuna cewa duk da irin kashe-kashen da ke faruwa a Borno, an samu ingantuwar zaman lafiya a Borno da yankin arewa maso gabas, mu na da shaidu a kan hakan.

KARANTA: Ganduje ya buƙaci Jami'ar Amurka ta bashi haƙuri kan naɗin muƙamin Farfesan bogi

"Alal misali, kafin hawan Buhari akwai adadin wasu kananan hukumomi da ba sa shiguwa, amma yanzu jama'a da sarakunansu sun koma garuruwansu da suka hada da Bama, Gwoza, Askira-Uba, Dikwa, Ngala, Monguno, Kukawa, Damboa, Konduga, Mafa, wadanda dukkansu wurare ne da basa shiguwa a wasu shekaru a baya.

"Kafin hawan Buhari kusan dukkan sarakunanmu sun yi gudun hijira. A yau, Bama ta dawo, haka Askira-Uba, Damboa, Gwoza, da sauransu sun dawo hayyacinsu. Yanzu haka harkoki har a Baga ma sun fara dawowa. Hakan bai yiwu ba sai bayan zuwan Buhari.

"Hatta a cikin Maiduguri akwai damuwa da kalubale wajen zirga-zirga, 'yan ta'adda suna kai hari sansanin sojoji; sun kai hari barikin sojoji a Monguna, Bama, Giwa da hedikwatar rundunar tsaro ta hadin gwuiwa (MJTF) da ke Baga da sauransu."

Legit.ng ta wallafa rahoton cewa tsohon dan majalisa a Jamhuriya ta biyu, Dattijo Dakta Mohammed Junaid, ya ce ba za'a taba samun zaman lafiya a Najeriya ba matukar shugaba Buhari da APC suna kan mulki.

A cewarsa, batun gyaran Najeriya fa ya fi karfin shugaban kasa, Muhammadu Buhari.

Dakta Junaid ya bayyana hakan ne yayin da yake martani a kan kisan manoma 43 da mayakan Boko Haram suka yi wa yankan rago a jihar Borno.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng