Zanga-zanga: Kamfanin Atiku, INTELS, ya kori ma'akata 700, ya hanasu hakkinsu
Sama da ma'aikatan kamfanin INTELS 700 da aka sallama sun yi zanga-zanga, suna neman hakkinsu.
Ma'aikatan da aka kora sun fara zanga-zangan tun ranan Talata kuma sun ce ba zasu daina ba har sai an biyasu hakkinsu, Vanguard ta ruwaito.
Masu zanga-zangan wadanda mambobin kungiyar ma'aikatan tashohon jirgin ruwa ne AMS, sun tare kofar shiga kamfanin rike da takardu masu rubuce-rubuce a kai.
Suna masu cewa, "Ku yi abinda ya dace na biyansu kudin kora, 'Kowani dan kwadago na da hakkin albashinsa, ku biyamu kudadenmu' ku taimaka INTELS' kada ku kora mu gida ba komai, ku tuna mu ma'aikatanku ne"
Yayin jawabi, shugaban kungiyar ma'aikatan, Sunday Atakpo, ya yi kira ga shugabannin INTELS su biya ma'aikatan da kudin sallama.
"Abinda suke yi ya sabawa dokokin kwadago. Su biya mutanenmu idan suna son mu rabu da su. Baku biyasu kudin sallama ba amma kuna koransu. Wannan abin kunya ne," yace.
Shugaban kungiyar kananan ma'aikatan INTELS, Tunde Bolaji, ya yi kira ga gwamnan jihar Rivers, Nyesom Wike; gwamnatin tarayya da kungiyoyin kwadago su sanya baki INTEL ta biya ma'aikatan kudadensu kafin sallamansu.
Asali: Legit.ng