Dauda Birmah: Wazirin Garkida, tsohon dan takarar shugaban kasa, ya rasu

Dauda Birmah: Wazirin Garkida, tsohon dan takarar shugaban kasa, ya rasu

- Alhaji Sauda Birmah, tsohon ministan ilimi kuma tsohon dan takarar shugaban kasa, ya rasu ranar Talata

- Marigayi Dauda Birmah ya taba rike mukamin ministan ilimi na kasa a lokacin mulkin marigayi Janar Sani Abacha

- Kazalika, sau biyu yana neman takarar kujerar shugaban kasa a tsohuwar jam'iyyar APP da ANPP

Allah ya yi wa toshon ministan ilimi kuma tsohon dan takarar shugaban kasa, Alhaji Dauda Birmah, rasuwa da safiyar ranar Talata, kamar yadda dan sa ya wallafa a shafinsa na Facebook kafin daga baya jikarsa ta sanar a shafinta na Tuwita.

Musa Dauda Birmah ya wallafa a shafinsa na Facebook cewa, "Inalillahi wa inna ilaihin rajiun, na rasa wani bangare na rayuwata da ba za'a taba samun madadinsa ba. Allah ya yafe zunubanka ya saka ka a Aljannah.

KARANTA: Adadin mutanen da kowacce jiha ta rasa sakamakon ayyukan ta'addanci a 2020

Kazalika, wani mai suna Ameen (@ameen_amshi) a dandalin sada zumunta na tuwita ya wallafa cewa, "Inalillahi wa Innailaihi rajiun, na rasa kakana, Alhaji Dauda Birmah, da safiyar yau. Za'a yi jana'izarsa a mahaifarsa, garin Garkida, a Jihar Adamawa. Allah ya jikan shi Ameen"

KARANTA: Kaduna: 'Yan bindiga sun kashe jarirai uku a harin da suka kaiwa 'yan tawagar biki

Dauda Birmah: Wazirin Garkida, tsohon dan takarar shugaban kasa, ya rasu
Dauda Birmah: Wazirin Garkida, tsohon dan takarar shugaban kasa, ya rasu Hoto: (@ameen_amshi, @dateline.ng)
Asali: Twitter

An haifi marigayi Dauda Birmah a ranar 21 ga watan Yuli na shekarar 1940 a garin Garkida da ke yankin karamar hukumar Gombi, jihar Adamawa.

Kafin rasuwarsa, marigayi Dauda Birmah ya rike mukamai da dama a tsohuwar gwamnatin arewacin Nigeria da kuma gwamnatin tarayya, sannan shine wazirin Garkida.

Ya taba rike mukamin ministan ilimi na kasa a karkashin mulkin tsohon shugaban kasa a lokacin soji, marigayi Janar sani Abacha.

Legit.ng ta rawaito cewa wata mata yar Najeriya ta sha alwashin matuƙar mijin ta ya nemi da su yi gwajin jinin ƴaƴansu na DNA, to tabbas kamar ya nemi takardar saki ne, kamar yadda The Nation ta rawaito.

Matar mai suna Mrs Eniola Carolina Herrera wacce ta tofa albarkacin bakinta ta shafinta na Tuwita kan batun da ake ta cacar baka a kafafen yaɗa zumunta na zamani, ta sha alwashin rabuwa da mijinta matuƙar ya buƙaci da su yi gwajin DNA.

Ana yin gwajin DNA ne domin tabbatar da hakikanin mahaifin yaro, yarinya, ko yara.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel