Gobara a Kano ta kone dukiya sama da N635m
- Hukumar kashe gobara ta jahar Kano ta ba da bayanin adadin kudi da rayukan da a ka rasa
- Hukumar ta bayyana wa manema labarai cewa tana shirin horar da sababbin ma'aikata
- Hukumar ta kuma shawarci iyaye da su kula da 'ya'yansu masu kananan shekaru
Hukumar kashe gobara ta jihar Kano ta ce an yi asarar rayuka 134 da dukiyoyi na kimanin N635m a sakamakon gobara a jihar daga Janairu 1 zuwa Dec.31, 2020, Vanguard ta ruwaito.
Alhaji Saidu Muhammad, jami’in hulda da jama’a na hukumar ya fadi haka lokacin da yake zantawa da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN) a Kano ranar Talata.
Muhammad ya ce hukumar ta kuma ceci rayuka 1,077 da dukiyoyi na kimanin N2.56b a cikin gobara 786 a lokacin.
KU KARANTA: Da alamun za a je aikin Hajji bana
“Mafi yawan barkewar gobarar ta samo asali ne daga rashin kulawa da sarrafa gas din girki, amfani da kayan lantarki marasa karfi da kuma rashin waya mai kyau a gidaje.
“Kimanin rayuka 134 da dukiyoyi na kimanin Naira miliyan 635 ne suka salwanta a gobarar a wannan lokacin da ake dubawa,” in ji shi.
Muhammad ya ce, masu aikin sun dauki kiran ceto guda 693 da kuma kiran karya guda 184 a lokacin.
Ya ce hukumar tana shirin horar da ma'aikata 350 a 2021 don yin aiki mai kyau.
Muhammad ya shawarci mazauna da su kula da wuta ko yaushe tare da kiyayewa don hana barkewar gobara.
KU KARANTA: Ma'aikata sama da 300 ba a biyansu albashi a Majalisar Dokoki
"Iyaye su guji tura yara masu kananan shekaru don diban ruwa daga rijiyoyi, koguna ko kududdufai su kadai." (NAN)
A wani labarin, Wata gobara da ta tashi da misalin ƙarfe 8 na daren ranar Laraba, ta yi sanadin ƙona shaguna sama da 150 a garin Funtua, jihar Katsina.
Wakilin Legit.ng Hausa, Sani Hamza Funtua wanda ya ziyarci kasuwar da gobarar ta faru, ya ruwaito cewa, gobarar ta jawo asarar dukiyar ƴan kasuwa, da kuɗin su ya zarce miliyoyin Naira.
Da ya ke zantawa da jaridar Legit.ng Hausa, shugaban ƴan kasuwar na bakin babban asibitin Funtua (SMASH), Alhaji Mujitafa Ibrahim, ya bayyana cewa, wannan ne karo na kusan uku da gobarar ta ke tashi a kasuwar, lamarin da ke jefa ƴan kasuwar a wani hali.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng