'Yan sanda sun hana yin casun badala a Adamawa

'Yan sanda sun hana yin casun badala a Adamawa

- Yan sanda sun hana faruwar wani casu na "Yola Beach Party" da aka shirya bisa zargin badala

- Hukumar ta ce tana gudanar da bincike don gano wanda suka shirya tare da daukar nauyin bikin

- A baya bayan nan gwamnatin Kaduna ta rushe wani wurin shakatawa bisa zargin shirya taron badala

A wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi, Sulaiman Yahaya Nguroje, mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar, ya ce akwai damuwar nuna tsiraici a wajen wasannin, The Cable ta ruwaito.

Nguroje ya ce duk wanda aka kama da aikata irin wannan laifi za su kai shi kotu.

"Mun hana wannan taron don kare martaba, al'ada, kima da kuma darajar jihar, duk wanda muka kama da hada irin wannan taruka ko aikata irin wannan laifi za a hukunta shi," in ji kakakin.

'Yan sanda sun hana casun 'badala' a Adamawa
'Yan sanda sun hana casun 'badala' a Adamawa. Hoto: @MobilePunch
Asali: UGC

DUBA WANNAN: Allah ya yi wa kanin sarkin Daura rasuwa sakamakon hatsarin mota

"An baza jami'ai don yin bincike ta karkashin kasa don gano su waye suka shirya taron, masu daukar nauyi da kuma inda aka shirya gudanar da taron."

Yan sanda sun ankara ne bayan da wata takarda ta yada ko ina dauke da rubutun "Yola Beach Party" da aka shirya gudanarwa karfe 2:00 na ranar 3 ga Janairu.

Ga duk mai son shiga zai biya naira 2,000 a matsayin kudin shiga kuma sai mutum ya shekara "18 ko fiye"

KU KARANTA: Zulum ya aza tubalin gina jami'a mai zaman kanta ta farko a Borno (Hotuna)

Za a yi raye-raye, ciye-ciye da sauran shagulgula.

Wannan na zuwa ne dai dai lokacin aka rushe Asher Kings and Queens Restaurant a Jihar Kaduna bisa irin wannan zargi.

Gwamnati ta ce ta rushe ginin ne bisa zargin shirya shagalin badala

A wani labarin daban, Sanata Elisha Abbo mai wakiltar mazabar Adamawa Ta Arewa a Majalisa ta 9 ya tabbatar da cewa zai yi takarar gwamna a Jihar Adamawa a shekarar 2023, The Punch ta ruwaito.

Abbo wanda ya bayyana hakan a Ganye kuma ya ce ya fice daga jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP, ne saboda jam'iyyar ta mutu.

A wurin gasar gano zakarun 'yan kwallon kafa da sashin matasa na kungiyar yakin neman zabensa ta shirya, mai suna Sanata Ishaku Abbo Ambassadors, (SIA Ambassadors), Abbo ya ce zai yi takarar kujerar gwamna a Adamawa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164