Bidiyon yadda luguden wutar sojoji ya halaka dumbin 'yan Boko Haram a Borno

Bidiyon yadda luguden wutar sojoji ya halaka dumbin 'yan Boko Haram a Borno

- Farmakin saman na rundunar sojin Najeriya ya yi sanadiyyar kashe ƴan ta'addan Boko Haram da dama, a cewar Hukumar Soji

- Jihar Borno, wacce ke yankin arewa maso gabas, ita ce cibiyar ayyukan Boko Haram tun shekarar 2009

- Manjo Janar Enenche, kakakin rundunar soji, ya ce mayakan kungiyar Boko Haram sun mutu da dama tare da lalata motarsu ta yaki

Hedikwatar Rundunar tsaron sojin Najeriya ta ce luguden sojojin sama (ATF) na Atisayen Lafiya Dole ya yi sanadiyyar kashe ƴan ta'addan ƙungiyar Boko Haram da dama tare da lalata motocin bindigunsu.

Rundunar soji ta ce hakan ya biyo bayan wani farmakin sama da sojoji suka kai wa mayakan kungiyar Boko Haram a Ajiri, ƙaramar Hukumar Mafa, jihar Borno.

Kakakin rundunar sojin Najeriya, Manjo Janar John Enenche, ne ya bayyana hakan a wani jawabi da ya fitar ranar Litinin a babban birnin tarayyar Najeriya, Abuja.

KARANTA: An wallafa hotunan wasu kayayyaki da Annabi Muhammad ya yi amfani da su

Bugu da kari, hedikwatar rundunar tsaro (DHQ) ta wallafa faifan bidiyon luguden wutar a shafinta na tuwita

Manjo Janar Enenche ya ce sojoji sun kai sumamen saman bayan samun bayanan cewa ƴan ta'addan sun yi fitar burgu a motocinsu masu bindigu, kuma sun yi yunƙurin shigowa gari cikin al-umma.

KARANTA: Covid-19: El-Rufa'i ya dauki sabon mataki da ya shafi ma'aikata, Masallatai da Coci

Ya ce cikin hanzari aka tashi jiragen yaƙin sojin saman Najeriya masu saukar ungulu don tunkarar ƴan ta'addan.

Bidiyon yadda luguden wutar sojoji ya halaka dumbin 'yan Boko Haram a Borno
Bidiyon yadda luguden wutar sojoji ya halaka dumbin 'yan Boko Haram a Borno @Thecable
Source: Twitter

Acewarsa, jiragen sojojin saman sun samu abin harinsu yadda ya dace, wanda hakan ya yi sanadiyyar sheƙe ƴan ta'addan tare da ruguza motocin bindigunsu.

Jihar Borno, Arewa maso gabashin Najeriya, itace gundarin cibiyar ayyukan ƴan ta'addan Boko Haram tun shekarar 2009.

Ayyukan ƙungiyar ta'addanci ta Boko Haram ya salwantar da rayuka da dama tare da tilasta mutane da dama yin hijira daga muhallinsu na ainihi.

Legit.ng ta rawaito cewa rundunar sojin Najeriya ta bayyana salon da ta bi na ceto yaran makarantar sakandire ta kimiyya dake ƙanƙara su 344 waɗanda yan ta'adda suka sace ranar 11 ga Disamba.

Kazalika, ta mayar da martanai ga ikirarin shugaban kungiyar Boko Haram, Abubakar Shekau, akan cewa kungiyarsa ce keda alhakin sace daliban.

A cewar rundunar Sojin, ta yi amfani da salo wajen kubutar da yaran don tabbatar da cewa babu wani yaro da aka kashe ko ya ji rauni a hannun 'yan ta'addar, kamar yadda rahotanni suka bayyana.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel