Ango ya dakatar da daurin aure bayan amarya ta yi katobara a 'Facebook'

Ango ya dakatar da daurin aure bayan amarya ta yi katobara a 'Facebook'

- Wata amarya ta ga 'ta leko, ta koma' bayan angonta ya dakatar da daurin aurensu da za'a yi a cikin watan nan

- Amaryar ta yi katobara wajen bayar da amsar cewa 'Eh' za ta iya cin amanar mijinta akan miliyan N1

Rahotanni sun bayyana yadda wani mutum dake dab da angwancewa da budurwarsa ya fasa aurenta sakamakon wani furuci da ta yi karkashin wani rubutu a kafar sada zumunta ta Facebook.

Matar dai ta je ƙarƙashin wani rubutu ne inda wani mutum ya jefa tambaya da cewa: "Shin za ki iya cin amanar mijin ki akan Naira miliyan ɗaya?"

A martanin matar wacce ke shirin amarcewa a cikin wannan watan na Disambar 2020 da muke ciki, ta bayar da amsar cewa "Eh" ga tambayar da aka yi.

KARANTA: Harin Jakana ya fusata Zulum, ya yi wa rundunar soji wata tambaya mai muhimmanci

An yi rashin sa'a wani da ya san matar ya kuma san wanda ke shirin auren ta, ya ɗauki hoton amsar da ta bayar; wato (screenshot), sannan ya turawa mutumin.

Ango ya dakatar da daurin aure bayan amarya ta yi katobara a 'Facebook'
Ango ya dakatar da daurin aure bayan amarya ta yi katobara a 'Facebook'
Asali: Original

Ganin hakan ne ya tashi hankalin angon har daga bisani ya ce shi ya hakura, ya fasa aurenta.

Ga yadda wata mai amfani da dandalin tuwita ta bayar da labarin;

"Wani mutum ya dakatar da daurin aurensa da za'a yi a cikin watan Disamba na shekarar 2020...saboda amaryar da za'a sha biki da ita ta bayar da amsar cewa za ta iya cin amanar mijinta akan miliyan daya ga tambayar da wani mutum ya yi a Facebook.

KARANTA: Bidiyon yadda luguden wutar sojoji ya halaka dumbin 'yan Boko Haram a Borno

"Shi kuma wani mutum da ya san wanda zai aureta sai ya dauki hoton wurin amsar da ta bayar ya nunawa ango....shin wannan mutum ya kyauta? Lagos."

Kalli rubutun;

Legit.ng ta rawaito cewa rundunar sojin Najeriya ta bayyana salon da ta bi na ceto yaran makarantar sakandire ta kimiyya dake ƙanƙara su 344 waɗanda yan ta'adda suka sace ranar 11 ga Disamba.

Kazalika, ta mayar da martanai ga ikirarin shugaban kungiyar Boko Haram, Abubakar Shekau, akan cewa kungiyarsa ce keda alhakin sace daliban.

A cewar rundunar Sojin, ta yi amfani da salo wajen kubutar da yaran don tabbatar da cewa babu wani yaro da aka kashe ko ya ji rauni a hannun 'yan ta'addar, kamar yadda rahotanni suka bayyana.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel