Abu daya za ka gaggauta yi idan kana kishin Nigeria; Ndume ya shawarci Buhari
- Ali Ndume, sanatan Jihar Borno ta kudu, ya shawarci shugaba Buhari ya yi sauye-sauye a kunshin gwamnatinsa
- Sanata Ndume ya ce shugaba Buhari mutumin kirki ne da ke da kyakyawar niyya amma akwai masu mugun nufi a tattare da shi
- A cewar Sanata Ndume, shugaba Buhari ya kafa tarihi a bangaren aiwatar da kasafin kudin kasa
Sanata mai wakiltar Borno ta Kudu kuma shugaban kwamitin soji na majalisar dattijai, Mohammed Ndume, ya buƙaci shugaba Muhammadu Buhari da ya yi canje-canje a gwamnatinsa matuƙar yana nufin Najeriya da alheri a shekarar 2021.
Sanatan ya yi wannan furucin ne jiya Litinin yayin da yake ganawa da yan jaridu a gidansa da ke Maiduguri babban birnin jihar Borno.
Koda ya ke ya ce shugaba Buhari mutum ne nagari amma akwai waɗanda ke ƙoƙarin kawo cikas ga yunƙurinsa na inganta rayuwar yan Najeriya.
KARANTA: An sace matan aure biyu, an kashe mutane 18 a Kaduna
Sanata Mohammed Ndume ya ce "Ina matuƙar farin ciki da aiwatar da kasafin 2020 da kusan kaso 90, nasarar da ba'a taɓa samu ba a tarihin ƙasar nan."
"Abin baƙin ciki kuma shine hakan bai taɓa wasu guraren da ya kamata ba musamman a yankin arewa maso gabas saboda rashin wakilci da mukamai marasa amfani."
Da ya ke magantuwa kan nasarorin da ya cimma a yankin da ya ke wakilta, sanatan ya ce daga 2019 zuwa yanzu, karo na huɗu da aka zaɓe shi, yana cikin waɗanda suka fi kowa samun nasarar aiwatar da kudirorinsu a mazaɓunsu.
A baya Legit.ng ta rawaito cewa Toshon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya janye dukiyar daga kamfanin Intels bayan ya zargi gwamnatin shugaba Buhari da yunkurin kashe masa kasuwanci.
Atiku ya fadi hakan a cikin jawabin da kakakinsa ya fitar domin sanar da cewa ya sayar da hannayen jarinsa a kamfanin 'Intels'.
Hukumar NPA na zargin kamfanin 'Intels' da kin bawa gwamnati kudaden haraji $48m da ya karba amadadin FG a shekarar 2017.
Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng