Atiku ya janye kudinsa daga kamfanin Intels, ya zargi Buhari da lalata masa kasuwanci
- Toshon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya zargi gwamnatin shugaba Buhari da yunkurin kashe masa kasuwanci
- Atiku ya fadi hakan a cikin jawabin da kakakinsa ya fitar domin sanar da cewa ya sayar da hannayen jarinsa a kamfanin 'Intels'
- Hukumar NPA na zargin kamfanin 'Intels' da kin bawa gwamnati kudaden haraji $48m da ya karba amadadin FG a shekarar 2017
Atiku Abubakar, tsohon mataimakin shugaban kasa, ya sayar da dukkan hannayen jarinsa da ke kamfanin 'Intels' mai jigila da safarar kayayyaki ta tashoshin ruwa, kamar yadda TheCable ta rawaito.
Da ya ke magana ranar Litinin, Atiku ya bayyana dole ce ta sa shi janye hannayen jarinsa daga Intels saboda gwamnatin Buhari ta nace sai ta durkusar da kamfanin tun bayan hawanta mulki a 2015.
Atiku ne tare da hadin gwuiwar wasu turawa suka kafa kamfanin 'Intels' mai harkokin jigila da safara ta ruwa da kuma kasuwancin fetur da gas.
KARANTA: Sanata Shehu Sani: Abubuwa 10 da duk mai sha'awa ko burin shiga siyasa a Nigeria ya kamata ya sani
A shekarar 2010 ne kamfanin 'Intels'ya shiga wata yarjejeniya ta karbar haraji a tashoshin jiragen amadadin gwamnatin tarayya.
Sai dai, tun bayan lokacin ake samun matsala a tsakanin kamfanin da gwamnatin tarayya bisa zargin 'Intels' da kwangen kudaden haraji.
A wani jawabi da Paul Ibe, kakakin Atiku, ya fitar ranar Litinin, tsohon mataimakin shugaban kasar ya zargi gwamnatin tarayya da yunkurin durkusar da bangaren kasuwanci.
KARANTA: Adawar siyasa: Fadar shugaban kasa ta radawa jam'iyyar PDP sabon sunan wulakanci
Gwamnatin tarayya na zargin kamfanin 'Intels' da rashin damka mata kudaden haraji da ya karba a shekarar 2017.
Hukumar kula da tashoshin jiragen ruwa na kasa (NPA) ta ce kamfanin 'Intels' ya gaza bawa gwamnati kimanin Dala miliyan $48m da ya karba a matsayin haraji a shekarar 2017.
Ibe ya bayyana cewa tun wasu shekaru da suka gabata Atiku ya fara sayar da hannayen jarinsa na kamfanin 'Intels'.
Legit.ng ta rawaito cewa tsohon sanata, Kwamred Shehu Sani, ya zayyano wasu abubuwa har 10 da duk wani dan Najeriya zai shiryawa kafin ya shiga siyasa.
Sanata Shehu Sani ya sha kaye a babban zaɓen da ya gabata na shekarar 2019 baya hamayyarsa da gwamna El-Rufa'i ta tilasta shi barin APC.
A cewar tsohon Sanatan, jerin abubuwa 10 shawara ce ga duk wani mutum da ya neme ya ba shi kafin ya tsunduma siyasa.
Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng