Nijeriya ba za ta taba gazawa ba - Gwamnatin Tarayya

Nijeriya ba za ta taba gazawa ba - Gwamnatin Tarayya

- Lai Mohammed ya bayyana cewa Najeriya ba zata taba zama kasar da zata gaza ba

- Ya kuma jaddada cewa kasar na da samun ci gaba wajen yaki da 'yan fashi da barayi

- A kalubalen da ya yi wa wata jaridar waje, ya bayyana ci gaba da aka samu na tsaro a wadannan shekaru

Gwamnatin Tarayya ta fada a ranar Litinin cewa Najeriya ba ta gaza ba kuma ba za ta taba gazawa ba.

Ministan yada labarai da al’adu, Alhaji Lai Mohammed ya bayyana hakan a wani taron manema labarai a Legas.

Financial Times ta Landan a ranar 22 ga watan Disambar da ta gabata ta gabatar cewa Najeriya na cikin hatsarin zama kasar da ta gaza sakamakon lamuran sace-sace da 'yan fashi

Amma Ministan ya kalubalanci babbar jaridar kasuwanci, yana mai cewa Najeriya "ba za ta iya zama kasar da ta gaza ba."

KU KARANTA: Gwamnatin jihar Gombe zata dawo biyan ƙarancin albashi nan kusa

Nijeriya ba za ta taba gazawa ba - Gwamnatin Tarayya
Nijeriya ba za ta taba gazawa ba - Gwamnatin Tarayya Hoto: Facebook/Lai Mohammed
Asali: Facebook

A cewar Mohammed, Najeriya na samun ci gaba matuka wajen magance barayi da satar mutane.

Ya jaddada cewa hasashen mummunan abu game da Najeriya ba zai cika ba, yana mai tuna cewa wasu masu sharhi na karya sun yi hasashen cewa Najeriya za ta shiga cikin shekaru 20 da suka gabata.

"Wannan bai faru ba kuma ba zai faru ba," in ji shi, ya kara da cewa Gwamnatin Tarayya ta samu ci gaba sosai wajen magance rashin tsaro kamar yadda ake gani tare da bukukuwan Kirsimeti da Sabuwar Shekara cikin lumana.

Ya tunatar da cewa a shekarar 2010 da 2011, hare-haren bama-bamai na Kirsimeti da sabuwar shekara sun yi sanadiyyar mutuwar mutane da jikkata da dama amma yanzu ba haka batun yake ba, yana mai bayar da tabbacin cewa Gwamnatin Tarayya za ta ci gaba da yaki da ta'addanci da satar mutane.

Mohammed ya bayyana shekarar 2020 a matsayin shekara mai matukar kalubale saboda annobar COVID-19, da zanga-zangar #EndSARS da kuma "tsananin rashin tsaro."

KU KARANTA: Rashin Tsaro: Buhari ya yi kira ga daukar matakin bai daya kan 'yan ta'adda

Sai dai ya bayar da tabbacin cewa kasar za ta samu ci gaba mai kyau a shekarar 2021 kuma ta fita daga matsin tattalin arzikin da take ciki a yanzu ta hanyar ayyukan gwamnati da dama a bangarori da dama na tattalin arziki.

“Mummunan Hasashe game da Najeriya ba zai cika ba. Najeriya ba za ta zama kasar da ta gaza ba, amma za ta tashi ne don zama kasar da ake girmamawa a cikin wasu kasashe,” in ji shi

A wani labarin daban, Shugaba Muhammadu Buhari ya ce "Yanzu ta'addanci ya zama kamar wata muguwar cuta wacce za ta iya yaduwa a kowane lokaci matukar ba a dauki mataki na bai daya ba."

Shugaba Buhari ya bayyana haka ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Garba Shehu ya fitar ranar Lahadi don mayar da martani kan kisan mutane 70 a garin Zaroumdareye, wani garin kan iyaka tsakanin Jamhuriyar Nijar da Mali da ‘yan bindiga suka yi, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Shugaban wanda ya yi Allah wadai da lamarin tare da nuna damuwarsa ga yadda tsaro yake qara tabarbarewa, ya ce wannan wani karin kira ne na daukar matakin bai daya na shugabannin Afirka kan ta'addanci.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.