Kano: Rundunar 'yan sanda ta kamo aljani bayan wani mutum ya shigar da kararsa (bidiyo)

Kano: Rundunar 'yan sanda ta kamo aljani bayan wani mutum ya shigar da kararsa (bidiyo)

- Wani aljani ya fada komar rundunar 'yan sandan jihar Kano bayan wani matashi mai suna Aliyu ya shigar da kararsa

- Aliyu ya bayyana cewa aljani ta waya ya fara kiransa tare da bashi tsoro kimanin shekaru uku da suka gabata

- An samu kudin bogi da wasu kayan tsatsiba a wurin aljanin da aka kama wanda kuma shine ya ke kiran Aliyu tare da tilasta shi yi wa aljanu hidima

Rundunar 'yan sanda a jihar Kano ta samu nasarar kama wani aljani bayan wani matashi mai suna Aliyu Haruna Usman ya shigar da kararsa.

A wani faifan bidiyo da kakakin rundunar rundunar 'yan sandan Kano, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya yi magana, mai korafi ya bayyana yadda abin ya faru.

DSP Kiyawa ya bayyana cewa mai korafin ya shafe tsawon shekaru uku yana hidimatawa wannan aljani ta hanyar yi masa dafgen naman kan shanu, farfesun kaji, kindirmo.

KARANTA: Dan majalisa ya kira taron manema labarai, ya sanar da sakin matarsa saboda ta sauya jam'iyya

Da yake magana da bakinsa a cikin faifan bidiyon, Aliyu ya bayyana cewa a wasu lokutan akan sanar da shi cewa 'ya'yan aljanu sun raina kayan alatun da ya kawo.

Kano: Rundunar 'yan sanda ta kamo aljani bayan wani mutum ya shigar da kararsa (bidiyo)
Kano: Rundunar 'yan sanda ta kamo aljani bayan wani mutum ya shigar da kararsa (bidiyo) @Solacebase.ng
Asali: Twitter

A cewarsa, aljanin; wanda ya fara kiransa ta lambar waya, ya tsoratar da shi idan bai yi abinda aljanu suke so ba za'a kone masa gida ko kuma ya mutu.

Kazalika, ya sanar da cewa aljanin ya shaida masa cewa idan ya jure, ya cigaba da yin hidima zasu yi masa sakayya, su azurta shi.

KARANTA: Manyan al'amuran siyasa 5 da suka yamutsa hazo a shekarar 2020

"Haka na cigaba da yin wahala har akwai lokacin da aljani ya kusa ya dakeni saboda na kai dafaffen nama kadan," a cewar Aliyu.

Sai dai, bayan ya shafe shekaru uku yana hidimatawa wannan aljani da ahalinsa, sai suka bashi kudin bogi.

Aliyu ya bayyana cewa bayan ya karbi kudin bogin, sai ya kawowa rundunar 'yan sanda tare da lambar wayar aljanin.

A baya Legit.ng ta rawaito cewa Babban sifetan rudunar 'yan sanda (IGP), Mohammed Adamu, ya nada sabbin manyan mataimakansa (DIGs) biyar.

Kazalika, ya bayar da gurbin aiki ga kowanne daga cikin manyan jami'an guda biyar da aka nada mukamin DIG.

IGP Adamu ya bukaci sabbin manyan 'yan sandan su yi aiki da kwarewarsu ta aiki wajen kawo sauyi mai ma'ana a rundunar 'yan sanda.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng