El-Rufa'i ya sauke sakatarorin ilimi 23, ya sauke shugaban CSDA, ya nada Sauda Ayotebi
- Nasir El-Rufa'i, gwamnan Kaduna, ya sauke sakatarorin ilimi na kananan hukumomin jihar 23
- Kazalika, gwamnan ya sauke shugaban hukumar CSDA tare da maye gurbinsa da Sauda Amina-Ayotebi
- Gwamnan ya ce an yi sauye-sauyen ne domin inganta aikin gwamnati a jihar Kaduna
Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa'i, ya sauke dukkan sakatarorin ilimi na kananan hukumomi 23 da ke Kaduna.
A cikin sanarwar da mai taimakawa El-Rufa'i a kan yada labarai da sadarwa, Muyiwa Adekeye, ya fitar ya bayyana cewa gwamnan ya sauke shugaban hukumar CSDA.
A cewar sanarwar, gwamna El-Rufa'i ya bayyana cewa an yi sauye-sauyen ne domin kawo gyara da inganta ayyukan gwamnati a jihar Kaduna.
Sanarwar ta kara da cewa El-Rufa'i ya nada Saude Amina-Atoyebi a matsayin shugabar riko, janaral manaja, a CSDA.
"Manyan jami'ai a bangaren ilimi a kananan hukumomi za su rike ofishin sakatarorin da aka sauke har zuwa sanar da nada sabbi," a cewar sanarwar.
KARANTA: An wallafa hotunan wasu kayayyaki da Annabi Muhammad ya yi amfani da su
Wani bangare na sanarwar ya bayyana cewa, "Saude ta fara aikin gwamnati a shekarar 2015 bayan gwamna El-Rufa'i ya nada ta a matsayin mai bayar da shawara kafin daga bisani a nada ta a matsayin mai kula da bangaren walwala a 2019.
"Saude ta yi digiri a ilimin tsimi da tanadi a jami'ar ABU Zaria, kusa da mahaifarta Wusasa, kafin daga bisani ta yi digiri na biyu a jami'ar Coventry da ke Ingila."
A baya Legit.ng ta rawaito cewa gwamnatin jihar Kaduna ta kara dauki mataki na gaba bayan sanar da rufe makarantu da wuraren taron biki da gidajen rawa.
A wani sako da gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa'i, ya fitar ya sanar da cewa ma'aikata kasa da mataki na 14 su cigaba da zama a gida.
Kaduna na daga cikin jihohin da ake ake samun hauhawar alkaluman masu kamuwa da korona a kowacce rana a 'yan kwanakin baya bayan nan.
Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng