Mahara sun yanka wani mafarauci a Abuja

Mahara sun yanka wani mafarauci a Abuja

- Wasu mahara sun yi wa mafarauci yankan rago a Chiji da ke Abaji, cikin birnin Abuja a yayin da ya fita farauta

- Wani dan uwan mamacin ya bayyana cewa wuka suka yan danuwansa da shi kuma babu alamar harsashi

- Rundunar 'yan sandan babban birnin tarayya Abuja ta ce tana bincike akan lamarin da nufin gano bata garin

Wasu mahara sun yanka wani mafarauci mai shekara 47, Mista Wabari Ukpaka, a yankin Chiji da ke unguwar Abaji a birin Abuja, Daily Trust ta ruwaito.

Wani mazaunin yankin, wanda ya bukaci a sakaya sunan shi ya ce lamarin ya faru ranar Alhamis din da ta wuce, bayan marigayin ya bar gida da misalin 4:00 na yamma don zuwa farauta a dajin da ke yankin.

Mahara sun yanka wani mafarauci a Abuja
Mahara sun yanka wani mafarauci a Abuja. Hoto: @daily_trust
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Yadda za a kawo karshen 'yan bindiga a Arewa, Gwamna Bagudu

Ya ce mamacin ya yi fakin din babur dinsa a gonarsa kuma ya shiga jeji don farutar nama da bindigarsa irin ta mafarauta amma wasu mahara suka kama shi kuma suka yi masa yankan rago.

"Iyalansa sunyi ta tsammanin dawowar sa da naman da ya farauto wanda za su yi bikin kirismeti, har zuwa yammacin juma'a, lokacin da aka gano yasasshiyar gawar sa da makwogwaran sa a yanke," a cewar sa.

Daya daga cikin iyalan mamacin ya shaida wa wakilinmu cewa babu alamar harsashi a jikin sa ya kuma kara da cewa maharan sunyi amfani da wuka mai kaifi wajen yanka wuyansa.

KU KARANTA: 'Yan bindiga sun kashe mutum 15, sun kone motocci 5 da shagun 11 a Kaduna (Hotuna)

"A takaice, babu alamar ciwon harsashi a jikin sa lokacin da muka je neman sa.

"Mun gano gawar sa an yanka makwogwaransa kuma an yar da gawar sa inda mutane zasu ganta cikin sauki," a cewar sa.

Da aka tuntubi mai magana da yawun rundunar yan sandan Abuja, ASP Maryam Yusuf, ta ce hukumar ta na bincike akan lamarin.

A wani labarin daban, Sanata Elisha Abbo mai wakiltar mazabar Adamawa Ta Arewa a Majalisa ta 9 ya tabbatar da cewa zai yi takarar gwamna a Jihar Adamawa a shekarar 2023, The Punch ta ruwaito.

Abbo wanda ya bayyana hakan a Ganye kuma ya ce ya fice daga jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP, ne saboda jam'iyyar ta mutu.

A wurin gasar gano zakarun 'yan kwallon kafa da sashin matasa na kungiyar yakin neman zabensa ta shirya, mai suna Sanata Ishaku Abbo Ambassadors, (SIA Ambassadors), Abbo ya ce zai yi takarar kujerar gwamna a Adamawa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel