Tambuwal ya sauke shugabannin kananan hukumomin Sokoto, ya fadi dalili

Tambuwal ya sauke shugabannin kananan hukumomin Sokoto, ya fadi dalili

- Aminu Waziri Tambuwal, gwamnan jihar Sokoto, ya sauke ilahirin shugabannin kananan hukumomin jihar Sokoto

- Tambuwal ya sanar da shugabannin kananan hukumomin cewa ya saukesu ne saboda dama na nadin kwarya ne

- Gwamnan ya ce duk mai son komawa kujerarsa zai iya shiga takara a fafata da shi a zaben kananan hukumomi mai zuwa

Gwamna Aminu Waziri Tambuwal na jihar Sokoto, ya rushe kafatanin shugabannin kantomomin riƙo na ƙananun hukumomi 23 dake faɗin jihar.

Gwamnan ya rushe kwamitin ne ran juma'a da ta gabata jim kaɗan da ganawarsa da su a gidan gwamnatin jihar ta Sokoto.

Ya bayyana gamsuwarsa bisa goyon baya da kwarin gwiwa da suka baiwa gwmanatinsa inda ya bayyana cewa "Duk kun yi iya ƙoƙarin ku don tabbatar da nasarar wannan gwamnati shekaru biyu baya da kuma bayan zaɓe."

KARANTA: Kano: Rundunar 'yan sanda ta kamo aljani bayan wani mutum ya shigar da kararsa (bidiyo)

"Duk kun san cewa ka'ida ta tsawon zangon mulkin ku shine wata shida, amma zuwa yanzu shekaru biyu kan karagar mulki,' in ji gwamnan.

Tambuwal ya sauke shugabannin kananan hukumomin Sokoto, ya fadi dalili
Tambuwal ya sauke shugabannin kananan hukumomin Sokoto, ya fadi dalili
Asali: Twitter

"Ina sane da wasun ku za su nemi tsayawa takara. Ina yi musu fatan alheri. Ko kun dawo ko ba ku dawo ba, za mu cigaba da tuntubar juna duk sanda buƙatar hakan ta taso."

KARANTA: Kano: Rundunar 'yan sanda ta kama kwararrun matasa barayin mota hudu, sunayensu

Cikin bayanin sa, tsohon shugaban ƙaramar hukumar gudanarwa ta Sokoto ta Arewa, Alhaji Aminu Ibrahim, da aka fi sani da No Delay, a madadin sauran takwararorinsa, bayyana godiya ya yi ga gwamnan bisa dama da ya ba su na yiwa jama'ar yankunansu aiki.

"Za mu cigaba da mara maka baya saboda mun fahimci manufarka ta son cigaban al'ummar jihar nan ne." In ji No Delay.

Legit.ng ta rawaito cewa Nasir El-Rufa'i, gwamnan Kaduna, ya sauke sakatarorin ilimi na kananan hukumomin jihar 23 watan Disamba, 2020.

Kazalika, gwamnan ya sauke shugaban hukumar CSDA tare da maye gurbinsa da Sauda Amina-Ayotebi

Gwamnan ya ce an yi sauye-sauyen ne domin inganta aikin gwamnati a jihar Kaduna.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel