An yi jana'izar Iyan Zazzau, Alh Bashar Aminu, a Zariya

An yi jana'izar Iyan Zazzau, Alh Bashar Aminu, a Zariya

- Masarautar Zazzau ta yi babban rashin da ba tayi irinta ba tun rasuwar marigayi sarkin zazzau, Alh Shehu Idris.

- An yi jana'izar mamatan biyu a cikin garin Zariya

- Shugaba Buhari ya aike sakon ta'azziyarsa ga masarautar Kano

An yi jana’izar marigayi Iyan Zazzau, Alhaji Bashar Aminu, yau Asabar 2 ga watan Janairu, 2021, misalin karfe 10 na safe a birnin Zariya, jihar Kaduna.

Dubunnan mutane sun halarci sallar jana’iza Iyan Zazzau wanda aka gudanar da babban Masallaci Juma’a karkashin jagorancin Babban Limamin Masarautar Zazzau, Liman Dalhatu Kasimu.

Bayan Sallar Jana'iza aka garzaya da gawar mamacin kuma aka birneshi a gidansa dake Sabon Gari GRA, Aminiya ta ruwaito.

KU DUBA: Rusa gidan casu: Majalisar koli ta Shari'ar Musulunci ta jinjinawa gwamna El-Rufa'i

An yi jana'izar Iyan Zazzau, Alh Bashar Aminu, a Zariya
An yi jana'izar Iyan Zazzau, Alh Bashar Aminu, a Zariya Hoto: @Aminiyatrust
Source: Twitter

KU DUBA: Sama da mutane 1000 sun kamu da cutar Korona ranar sabuwar shekara

Masarautar Zazzau ta yi babban rashin da ba tayi irinta ba tun rasuwar marigayi sarkin zazzau, Alha Shehu Idris.

Manyan masu sarauta biyu suka mutu ranar juma'a.

Yayinda Iyan Zazzau, Aminu, ya rasu a wani asibitin jihar Legas kuma aka kai shi Zaria domin jana'iza, Talban Zazzau, Iya-Pate, ya rasu ne a Zariya bayan rashin lafiyan da yayi fama da shi.

Mai martaba sarkin Zazzau, Ahmed Bamalli, ya fara sanar da mutuwar Iyan Zazzau a shafin Tuwita, ranar Juma'a.

"Cikin bakin ciki da alhini muke sanar da mutuwar mai sarauta mafi karfi kuma Yarima mafi arziki a arewacin Najeriya, Alha Bashar Aminu, Iyan Zazzau," yace.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel