Nasiru Kachalla: An kashe ƙasurgumin dan bindiga a dajin Kaduna

Nasiru Kachalla: An kashe ƙasurgumin dan bindiga a dajin Kaduna

- Fada tsakanin kungiyoyin yan bindiga biyu ya yi sanadiyar mutuwar gagarumin dan bindiga Nasiru Kachalla a Jihar Kaduna

-Kachalla ne wanda ake zargin shine kashin bayan ayyukan ta'addanci da dama a Jihar Kaduna da kewaye

- Ana zargin sa da aikata laifukan garkuwa da da dama ciki harda garkuwa da dalibai da malaman makarantar Engraves a Oktoban 2020

An kashe Nasiru Kachalla, Mashahurin dan bindiga, wanda ake zargin shine kashin bayan ayyukan ta'addanci da a Jihar Kaduna, inji gwamnatin Jihar Kaduna.

A wata sanarwa da Samuel Aruwan, kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida ya fitar ranar Litinin ya ce an kashe Kachalla a wata fafatawa tsakanin tawagar sa da kuma wata tawagar yan ta'addan.

Shi ne ke jagorantar ayyukan ta'addanci da dama ciki harda garkuwa da mutane, kashe kashe, satar shanu da sauran wasu da dama, HumAngle ta ruwaito.

An kashe kasurgumin dan bindiga Kacalla a Kaduna
An kashe kasurgumin dan bindiga Kacalla a Kaduna. Hoto: @HumAngle
Asali: UGC

DUBA WANNAN: Sirrin cin galaba kan 'yan bindiga a Arewa yana Zamfara, in ji Matawalle

A cewar Aruwan, masu binciken kwakwaf sun tabbatar da cewa an kashe yan ta'addan daya bangaren, da kuma wasu daga cikin sojojin Kachalla.

"Karawar ta afku a wani daji da ke kan iyakar kananan hukumomin Kajuru-Chikun na jihar Kaduna," ya bayyana a cikin sanarwar.

Aruwan ya yi bayanin cewa fadan ya barke akan wani garken shanu da aka sato.

Ya ce Kachalla da tawagar sa suna da hannu wajen ayyukan bata gari, ciki har da garkuwa da mutane, kashe kashe da kuma ta'addancin da ke faruwa kan titin Kaduna zuwa Abuja dama na Chikun/Kajuru.

KU KARANTA: Gwamnan Kano Ganduje ya yi wa Sanata Kwankwaso ta'aziyyar rasuwar mahaifinsa

Kwamishinan ya bayyana cewa Kachalla ne ya shirya garkuwa da mahalarta bitar da aka shiryawa makiyaya ranar 9 ga Janairun 2020 da kuma garkuwa da Mrs Bola Ataga da yayan ta guda biyu ranar 24 ga Janairun 2020.

"Daga bisani kuma yan ta'addan suka kashe daya daga cikin mahalarta taron, Michael Nnadi da Mrs Ataga kafin su saki yayan ta," a cewarsa.

Tawagar Kachalla ne dai ke da hannu wajen garkuwa da dalibai shida da kuma malamai biyu na makarantar Engravers College, a kauyen Kakau na karamar hukumar Chikun ranar 3 ga Oktobar 2019.

Ya ce yayin da jami'an tsaro ke neman Kachalla, sun Chafke yan tawagar sa uku, Tukur Usman, Shehu Bello da Mustapha Mohammed a watan Afrilun 2020.

A wani rahoton da Legit.ng ta wallafa, ministan tsaron Najeriya, Manjo Janar Bashir Salihi Magashi, ya bukaci kiristoci da su yi wa kasa addu'ar zaman lafiya lokacin bukukuwan zagayowar haihuwar Almasihu wato kirsimeti.

Janar Magashi ya mika rokon a sakon taya kiristoci murnar Kirsimeti da ya fitar ranar Alhamis 24 ga watan Disamba kamar yadda Channels Tv ta ruwaito. Kirstimeti: Ku yi wa sojoji addu'a don kawo karshen tashin tsaro, Ministan tsaro.

Ya bukaci kiristoci da su zama kamar Yesu yayin bikin haihuwar tasa ta hanyar kyautatawa yan uwansu yan Najeriya ba tare da la'akari da bambancin addini ba sannan su yi wa kasa addu'ar zaman lafiya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164