Harar tawaga: Sarkin Kauran Namoda ya karyata ikirarin 'yan sanda

Harar tawaga: Sarkin Kauran Namoda ya karyata ikirarin 'yan sanda

- Alhaji Sanusi Muhammad Asha, sarkin Kauran Namoda ya karyata ikirarin 'yan sandan jihar Katsina

- Ya ce ba 'yan sandan bane suka cece su ba, hasalima sai da aka yi sa'o'i biyu da yi wa mutanensa barna suka isa wurin

- Ya bayyana yadda dakarun sojin su ke Faskari suka isa Maska suka tsaya har sai safiya sannan suka tafi

Sarkin Kauran Namoda a jihar Zamfara, Manjo Sanusi Muhammad Asha ya musanta ikirarin rundunar 'yan sandan jihar Katsina inda suka ce sune suka cece shi yayin da 'yan bindiga suka kai masa hari a kan titin Zaria zuwa Funtua.

Sarkin ya sanar da Daily Trust cewa a yayin da aka kai masa hari kusa da garin Maska, babu dan sanda ko daya a yankin.

"A yayin da wasu daga cikinmu suka tsere, tawagata ta karasa wani kauye da ake kira Kwanar Maska inda muka tambaya ko akwai 'yan sanda amma suka ce babu sai mun karasa Funtua.

KU KARANTA: Saraki: Dalilin da yasa majalisa karkashin mulkina ta ki amincewa da wasu nade-naden Buhari

Harar tawaga: Sarkin Kauran Namoda ya karyata ikirarin 'yan sanda
Harar tawaga: Sarkin Kauran Namoda ya karyata ikirarin 'yan sanda. Hoto daga @Thecableng
Asali: UGC

"Na karasa Funtua inda na isa ofishin 'yan sanda sannan na gabatar da kaina. An sanar da ni cewa kwamandan yankin baya nan.

"Sai da nayi masa magana ta waya ne yace in yi magana da DPO wanda nayi ta waya. Daga nan aka bada motoci da jami'ai suka je dauko gawawwakin wadanda suka rasu.

“Hakan ta faru ne bayan sa'o'i biyu da kai man hari. Da kaina na kira Manjo Janar Aminu Bande wanda ya turo min dakaru daga Faskari.

"Daga isowarsu, kai tsaye suka wuce yankin inda suka tsaya har safiya amma abun alhinin shine yadda muka rasa rayukan mutum 8," basaraken yace.

KU KARANTA: Hadimin Aisha Buhari ya waske, ya ki bayyana inda uwargidan shugaban kasa take

A wani labari na daban, tsohon sanatan Kaduna ta tsakiya, Shehu Sani, ya ce 'yan majalisar wakilai suna tsoron shugaba Muhammadu Buhari, shiyasa suka soke gayyatar da suka yi masa.

Sani ya yi wannan maganar ne da BBC Hausa, inda yace ya kamata shugaba Buhari ya bayyana gaban majalisar don amsa tambayoyi a kan matsalolin tsaron dake addabar Najeriya.

A cewarsa, babu dalilin da zai sanya a ce su gayyaci Buhari kuma su koma su canja ra'ayi.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng