Dokar rajistar layi ta sa mutane miliyan 2 sun koma babu aikin yi inji ATOASDA

Dokar rajistar layi ta sa mutane miliyan 2 sun koma babu aikin yi inji ATOASDA

- Kungiyar ATOASDA ta nemi Gwamnati ta janye dokar rajistar layin waya

- ATOASDA ta ce miliyoyin matasa sun rasa hanyar cin abinci a dalilin dokar

- An yi kira ga hukuma ta bari a cigaba da saida layin wayar sulala a Najeriya

Kusan matasan Najeriya miliyan biyu su ka koma ba su da aikin yi a dalilin dakatar da rajista da saida layin waya da gwamnatin tarayya ta yi.

Jaridar Daily Trust ta rahoto wata kungiya ta na kokawa da wannan mataki da ma’aikatar sadarwa da tattalin arziki na zamani ta dauka.

Kungiyar Arewa Telecom Operators Agents and Simcard Dealers Association (ATOASDA), ta yi wannan ikirari da ta ke magana da ‘yan jarida.

AROASDA ta masu saida layin waya da rajista a Arewacin Najeriya ta bayyana cewa sabon tsarin da aka kawo ya kara yawan masu zaman banza.

KU KARANTA: NCC za ta rufe duk layin da bai da rajista

Shugaban wannan kungiya, Hassan Yakubu, ya yi jawabi a Kaduna, ya ce dokar cewa sai an hada layi da lambar NIN ya sa dinbin matasa ba su da abin yi.

Hassan Yakubu ya yi jawabi a madadin kungiyarsu mai cikakkiyar rajista da CAC/IT/NO131761.

Yakubu ya ce dole gwamnatin tarayya ta yi a hankali da wannan tsari da ta shigo da shi domin a sanadiyyar hakan, ta kara yawan masu zaman banza.

ATOASDA tace tana goyon bayan kokarin da gwamnati ta ke yi na kare rai da dukiyoyin al’umma.

KU KARANTA: Tasirin rufe iyokokin kasa da aka yi na shekara 1.5

Dokar rajistar layi ta sa mutane miliyan 2 sun koma babu aikin yi inji ATOASDA
ATOASDA ta ce miliyoyi sun dogara da saida SIM Hoto: Photo: scitechafrica.com
Asali: UGC

Malam Yakubu ya ce miliyoyin matasa ‘yan shekara 20 zuwa 40 ne su ka cika wannan harka ta sana’ar SIM inda su ke samun abin da za su ci duk wata.

Kungiyar ta bada shawarar a cigaba da saida layin waya, sannan a kara adadin masu yi wa mutane rajistar NIN a fadin kananan hukumomin kasar.

Kwanaki kun ji cewa a dalilin wannan doka da aka shigo da ita, layin wayoyin salular sama da mutum miliyan 160 su na fuskantar barazana a datse su.

Gwamnati ta ce dole a hada kowane layi da lambar NIN din mai ita. Amma masana su na ganin zai yi wahala a iya gama wannan kafin wa'adin ya cika.

Hukumar NCC a karkashin ma'aikatar Dr. Isa Ali Ibrahim Pantami ta shigo da wannan tsari.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng