Wajibi ne ku baiwa mutum sauran 'Data' da bai karasa ba idan ya siya wani ko tayi esfiya - NCC ga kamfanonin sadarwa

Wajibi ne ku baiwa mutum sauran 'Data' da bai karasa ba idan ya siya wani ko tayi esfiya - NCC ga kamfanonin sadarwa

- Tsugunnu bata kare ba kan yankan aljihun da kamfanonin sadarwa ke yiwa kwastamomi

- Sau tari hukumar NCC ta bukaci kamfanonin su rage kudin 'Data'

- A wannan karon, hukumar ta jaddadawa kamfanonin dokar baiwa kwastomomi ragowan 'Data' idan suka sabunta

Wajibi ne a baiwa mutum ragowan 'Data' da bai yi amfani da shi ba idan ya sake siyan wani, kamfanin sadarwan Najeriya NCC ta bayyana hakan.

Kakakin hukumar NCC, Ikechukwu Adinda, ya bayyana hakan a jawabin da ya saki ranar Alhamis, 17 ga Satumba.

Ikechukwu ya ce hukumar ta yanke shawarar hakan ne a zaman da tayi da manyan jami'an kamfanonin sadarwa kan koke-koken da mutane ke shigarwa.

Zaman da akayi ta yanar gizo, ya mayar da hankali ne kan jin dadin kwastomomi da kuma sauraron koke-kokensu.

"Hukumar na farin cikin jaddada cewa umurnin da ta bada a Yunin 2018 ga kamfanonin sadarwa cewa su rika baiwa mutane sauran 'Datansu' inda suka sayi wani." ya ce.

"Abinda ake nufi shine idan mutum bai karkare amfani da 'Data' ba har tayi esfiya, wajibi ne a daura masa kan sabo idan ya siya."

"Saboda haka hukumar tana kira da kamfanonin sadarwa sun ilmantar da kwastamomi kan yadda zasu yi amfana da hakan."

Hukumar NCC ta ce kamfanonin sadarwan sun amince da hakan kuma a rika duba lamarin koda yaushe.

DUBA NAN: Bayan shekaru 14 ana gini da rikicin hana ginawa, an kammala ginin Masallacin Juma'ar farko a kasar Greece

Wajibi ne ku baiwa mutum sauran 'Data' da bai karasa ba inda ya siya wani ko tayi esfiya - NCC ga kamfanonin sadarwa
NCC ga kamfanonin sadarwa
Source: Twitter

A watan Agusta, NCC ta yi kira ga kamfanonin sadarwa su rage kudin katin shiga yanar gizo da akafi sani da 'Data' saboda su ma an rage musu kudin lasisin birne wayoyinsu a jihohin Najeriya

Shugaba hukumar NCC, Farfesa Umar Garba Danbatta, ya bayyana hakan yayainda yake jawabi ga mahalartan taron yanar gizon majalisar masu amfani da layukan sadarwa, a hedkwatar NCC dake Abuja.

Danbatta ya ce dubi ga irin hobbasan da gwamnatin Najeriya tayi na ganin cewa an ragewa kamfanonin sadarwan kudin lasisin birne wayoyinsu a jihohi zuwa kasa da N145 ga mita yayinda wasu jihohi suka yafe kudin gaba daya, ya zama wajibi su dan yunkura domin nuna godiya .

"Hukumar na sa ran cewa dubi da ragin kudin lasisin birne wayoyin da aka samu, wanda zai rage kudin da kamfanonin sadarwa zasu rika kashewa, ya kamata su nuna godiya ta hanyar rage kudin abubuwa musamman 'data' ga yan Najeriya," Ya ce

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Tags:
Online view pixel