An fara gulma da tsegumi akan dalilin ganawar Buhari da Zulum a Villa

An fara gulma da tsegumi akan dalilin ganawar Buhari da Zulum a Villa

- A ranar Laraba ne Farfesa Babagana Umara Zulum, gwamnan Jihar Borno, ya ziyarci shugaban kasa, Muhammadu Buhari, a fadarsa

- Sai dai, fadar shugaban kasa da ofishin gwamna Zulum basu fitar da sanarwa dangane da ganawar ba

- Ma su hasashe na ganin cewa ganawar ba zata rasa nasaba da batun tsaro a Jihar Borno ba

A ranar Laraba ne shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya karbi bakuncin gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, a fadarsa, Villa, wacce ke Aso Rock a birnin tarayya, Abuja.

Hadiman shugaban kasa da kafafen yada labarai sun wallafa hotunan ziyarar da Farfesa Zulum ya kai wa Buhari a fadarsa.

Sai dai, babu wani karin bayani a kan dalilin ganawar, fadar shugaban kasa da ofsihin gwamna Zulum basu bayyana dalilin ganawar ba ya zuwa yanzu.

Jaridar Punch ta rawaito cewa duk da ganawar Buhari da Zulum ta sirri ce, ba za ta rasa nasaba da batun tsaro a Jihar Borno ba.

Jihar Borno ta kasance cibiyar harkokin kungiyar Boko Haram da takwararta ta ISWAP.

An fara gulma da tsegumi akan dalilin ganawar Buhari da Zulum a Villa
An fara gulma da tsegumi akan dalilin ganawar Buhari da Zulum a Villa
Source: Twitter

Gwamna Zulum bai yi magana da manema labarai a fadar shugaban kasa ba bayan ganawarsa da Buhari.

A iya ranar Asabar da ta gabata, rahotanni sun tabbatar da cewa an kashe akalla mutane uku a wani hari da mayakan kungiyar Boko Haram suka kai wasu kauyuka a yankin karamar hukumar Hawul.

Rahotanni sun bayyana cewa 'yan ta'addar sun lalata makarantu, wuraren ibada, da sauran wasu gine-gine a kauyuka hudu da suka kai hari.

KARANTA: Katsina: 'Yan bindiga sun koma cikin fushi bayan guduwar mutane 8 da suka sace, sun sake sace wasu 9

A baya Legit.ng ta rawaito cewa Farfesa Zulum ya ce duk da kisan manoma 43 da mayakan kungiyar Boko Haram su ka yi a Zabarmari, tsaro ya karu a jihar a karkashin mulkin shugaban kasa, Muhammadu Buhari.

Farfesa Zulum, ya bayyana hakan ne yayin da ya karbi bakuncin kungiyar dattijan arewa a karkashin jagorancin shugabanta, Ambasada Shehu Malami, da kuma sakatarenta, Audu Ogbeh.

Hakan na kunshe ne a cikin jawabin da gwamnatin jihar Borno ta fitar mai taken 'Zulum: Duk da kashe-kashe, shaidu a kasa sun nuna cewa an fi samun zaman lafiya a karkashin mulkin Buhari a Borno.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel