Obasanjo: Kar na sake jin wani ya dorawa Allah alhakin halin da muke ciki a Nigeria

Obasanjo: Kar na sake jin wani ya dorawa Allah alhakin halin da muke ciki a Nigeria

- Olusegun Obasanjo, tsohon shugaban kasa, ya yi kira ga 'yan Nigeria a kan su daina dora alhakin matsalolin kasa a kan Allah

- Obasanjo ya bayyana hakan ne a matsayin martani a kan kalaman shugaba Buhari a sakonsa na shiga sabuwar shekara

- A cewar tsohon shugabar, bai yarda Allah ne ya kaddara halin talauci da Nigeria ke ciki ba

Tsohon shugaban ƙasa, Olusegun Obasanjo, ya yi kira ga 'yan Najeriya da su yi aiki tukuru tare da yin addu'a domin samun nasarar ƙasar nan a sabuwar shekara mai kamawa, kamar yadda today.ng ta rawaito.

Obasanjo ya bayar da wannan shawara ne a dakin karatunsa mai suna Olusegun Obasanjo Presidential Library dake Abeoluta cikin jihar Ogun a wani sakonsa na shiga sabuwar shekara.

Ya kalubalanci shugaba Buhari da sauran shugabanni su daina dora alhakin halin da Najeriya ke ciki kan Ubangiji, su zargi kansu kurum.

KARANTA: Pantami Vs Dabiri, Malami Vs Magu da wasu sabani 3 da aka samu tsakanin hadiman Buhari

Obasanjo ya nuna ƙin amincewarsa cewa, Allah ne ya ƙaddara halin talauci da Najeriya ke ciki, inda ya dora alhakin hakan ga shugabannin da suka jefa ta cikin wannan mayuwacin halin.

Obasanjo: Kar na sake jin wani ya dorawa Allah alhakin halin da muke ciki a Nigeria
Obasanjo: Kar na sake jin wani ya dorawa Allah alhakin halin da muke ciki a Nigeria
Source: UGC

A cewarsa, "Bai kamata mu rinka dorawa Allah laifin halin da ƙasar mu ke ciki ba, dole mu zargi kanmu, Najeriya bai kamata ta zama talaka ba, bai kamata ɗan Najeriya ya kwanta da yunwa ba"

KARANTA: Korona 2.0: Za'a ji jiki a watan Janairu; NCDC ta gargadi 'yan Nigeria

"Halin da muke ciki zaɓi ne na shugabanni da mabiya. Addu'ata shine Ubangiji Ya sa shekarar 2021 ta zame mana alheri ga kowa, amma haka ba zai faru ba sai mun haɗa da aiki tukuru"

Ya sake jaddada bukatarsa ga yan Najeriya cewa matuƙar suna son tabbatar Najeriyar da suke so, wajibi ne su tashi aiki tukuru sannan su haɗa da addu'a, don tunkarar kalubalen dake gaba.

A baya Legit.ng ta rawaito cewa majalisar wakilan Najeriya ta fidda sanarwar ƙaryata neman afuwar Shugaba Buhari bisa gayyatarsa ya gurfana gaban majalisar don bayani kan matsalar tsaro da ta addabi ƙasa.

Sanarwar ta ƙaryata rahotannin da wasu kafafen yaɗa labarai ke fitarwa kan cewar ƴan majalisar za su roƙi afuwar Shugaban ƙasa bayan sun amince da ƙudirin gayyatarsa, kamar yadda BBC ta wallafa.

Wasu ƴan majalisa daga jihar Borno ne suka nemi a gayyato shugaba Buhari don ya yi bayani akan halin rashin tsaro da ake fama da shi.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel