Elisha Abbo ya sanar da dalilinsa na ficewa daga jam'iyyar PDP

Elisha Abbo ya sanar da dalilinsa na ficewa daga jam'iyyar PDP

- Sanata Elisha Abbo ya ce ya fita daga PDP ya koma APC ne don ya yi takarar gwamna a 2023 ya kada Gwamna Ahmad Fintiri

- Ya kuma ce dalili na biyu shine yadda gwamnan Jihar, Fintiri, ya janyo taɓarbarewar jam'iyyar PDP a jihar

- Har wa yau, Abbo ya ce baya fargabar gwamna Fintiri domin shine ya yi fafutikan ganin ya zama gwamna tunda farko

Elisha Abbo, Sanatan Jihar Adamawa da ya sanar da ficewarsa daga jam'iyyar PDP ya koma APC ya ce ya barwa gwamnan jiharsa, Ahmadu Fintiri jam'iyyar ne don ya maye gurbinsa a matsayin gwamna nan gaba.

Ya bayyana hakan ne yayin jawabin da ya yi wa manema labarai a ranar Laraba kamar yadda Premium Times ta ruwaito.

Mista Abbo ya sanar da ficewarsa daga jam'iyyar PDP ne cikin wasikar da shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan ya karanto yayin fara zaman majalisa.

Elisha Abbo ya sanar da dalilinsa na ficewa daga jam'iyyar PDP
Elisha Abbo ya sanar da dalilinsa na ficewa daga jam'iyyar PDP
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Jihohi 10 mafi arziki a Najeriya

Yan majalisar da dama musamman na APC sunyi ta murna yayin da ake karanto wasikar a zauren majalisar.

Ya kuma ce ya yanke shawarar barin PDP saboda rashin warware matsalolin da Gwamna Ahmadu Fintiri ya janyo a jam'iyyar reshen jihar wadda ya janyo rigingimu da dama.

"Don samun damar hidimta wa mutanen kirki na mazabar Adamawa ta Arewa, na fice daga PDP na koma APC daga yau Laraba 25 ga watan Nuwamban 2020," kamar yadda wani sashi na sanarwarsa ta ce.

Da aka masa tambaya kan ainihin dalilin da yasa zai bar PDP.

Ya amsa da cewa an rika samun matsalolin cikin gida a jam'iyyar tun lokacin da Fintiri ya zama gwamna.

KU KARANTA: Iyalan mai tallar jarida da aka kashe sun nemi naira miliyan 500 daga wurin kakakin majalisa

Ya ce gwamnan baya tayar masa da hankali domin yana daga cikin wadanda suka yi shiga suka fita wurin ganin ya zama gwamna a jihar.

"Hankali na bai tashi ba don nasan irin aikin da nayi don ganin Fintiri ya yi nasara. Ka je kayi bincike, ba cika baki na ke yi ba. Nine jigo wurin ganin Fintiri ya zama gwamna," in ji shi.

Abbo ya kara da cewa ƙaramar hukumarsa ta Mubi North ce ta biyu wurin yawan al'umma a jihar kuma dukkan jiga-jigan PDP daga yankin suka fito amma sun gaza kada shi don yana samun goyon bayan talakawa.

A wani labarin, Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Mohammad, ya ce yana jin daɗin jam'iyyar PDP kuma ba shi da wani shiri na komawa jam'iyyar APC kamar yadda Channels tv ta ruwaito.

A wata sanarwa ranar Juma'a, mai taimakawa gwamnan ɓangaren yada labarai, Mukhtar Gidado, ya ƙaryata zargin cewa uban gidansa na cikin jerin gwamnoni da zasu koma jam'iyya mai mulki.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164