2023: Sunayen shugabannin kamfen da Atiku ya kaddamar a jihohi 36

2023: Sunayen shugabannin kamfen da Atiku ya kaddamar a jihohi 36

- Tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar ya kaddamar da kungiyar kamfen

- An kaddamar da gagarumar kungiyar a ranar Alhamis a babban birnin tarayya da ke Abuja

- A kowacce cikin jihohi 36 da babban birnin tarayya, an nada shugaban kungiyar kamfen kafin 2023

Kafin zuwan zaben 2023, tsohon mataimakin shugaban kasan Najeriya, Alhaji Atiku Abubakar ya kaddamar da kungiyoyin goyon bayansa na kamfen a jihohi 36 na kasar nan.

An kaddamar da kungiyar a Abuja tare da Alhaji Abubakar Kabir Babawo a matsayin darakta janar da kuma Atiku Aminu Mohammed a matsayin shugaban kungiyar, The Nation ta wallafa.

KU KARANTA: Boko Haram: Zulum ya gana da shugaba Deby a kan 'yan gudun hijiran Borno a Chadi

2023: Sunayen shugabannin kamfen da Atiku ya kaddamar a jihohi 36
2023: Sunayen shugabannin kamfen da Atiku ya kaddamar a jihohi 36. Hoto daga @Thenation
Source: Twitter

Kudirin kungiyar kamar yadda aka gano shine kamfen ga tsohon mataimakin shugaban kasan domin samun hayewa shugabancin kasa a 2023.

Shugabannin kungiyoyin sun hada da Orngu Anngu, shugaban kungiyar na yankin arewa ta tsakiya; Isiaka Mogaji, mataimakin shugaban kungiyar na yankin arewa ta tsakiya.

Shugaban mata Mabe Ameh, shugaban kungiyar na jihar Benue, George Odoo Ezekiel; shugaban kungiyar na jihar Niger, Hassan Shuaibu Dada, shugaban kungiyar na jihar Kwara, Segun Olawoyin.

A jihar Kogi, shugaban kungiyar shine Ocheni Titus Okayi, shugaban kungiyar na jihar Nasarawa shine Abubakar Agwai, a babban birnin tarayya akwai Agajo Daniel da kuma jihar Filato, Solomon Ballason Shitnan.

KU KARANTA: 2023: Yarima ya bayyana kudirinsa na tsayawa takarar shugabancin kasa

A wani labari na daban, wani dan majalisar wakilai, Sam Onuigbo ya bar jam'iyyar PDP zuwa jam'iyya mai mulki ta APC, Premium Times ta wallafa.

Dan majalisar, mai wakiltar mazabar Ikwuano/Umuahia da ke jihar Abia, ya bayyana canja shekarsa ta wata wasika wacce kakakin majalisar, Femi Gbajabiamila, ya karanta a ranar Alhamis.

Kamar yadda aka saba, shugaban marasa rinjaye, Ndudi Elumelu ya bayyana rashin amincewarsa dangane da canja shekar Onuigbo, inda ya bukaci kakakin ya kwace kujerar, bukatar da bata samu karbuwa ba.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel