'Yan bindiga sun koma Sabuwa cikin fushi bayan guduwar mutanen da suka sace, sun sake sace wasu 9
- Yan bindiga sun sake kai hari garin Albasun Liman Sharehu da ke karamar hukumar Sabuwa a Jihar Katsina
- A hrin da suka kai na biyu, yan bindigan sun sake yin awon gaba da mutane guda tara don maye gurbin 8 da suka tsere
- Mutanen da aka yi garkuwar da su sun samu nasarar tserewa ne a yayin da 'yan bindigan da suka sace su ke sharbar barci
Wasu 'yan bindiga, cikin fushi, sun sake kai hari garin Albasun Liman Sharehu dake yankin karamar hukumar Sabuwa a Jihar Katsina tare da yin garkuwa da mutane tara.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa ‘yan bindigar sun sake kai harin kauyen ne da sanyin safiyar ranar Laraba.

Asali: UGC
Wakilin Daily Trust ya ruwaito cewa daga cikin mutanen da 'yan bindigar suka yi garkuwar da su akwai wani dalibin aji biyar a babbar sakandire ta Damari, wanda aka sace tare da mahaifinsa.
DUBA WANNAN: An yanke wa ƴan ta'adda 168 hukuncin ɗaurin rai-da-rai - Rahoto
Kafin wannan harin, 'yan bindiga sun kai hari kauyen a ranar Kirsimeti tare da yin garkuwa da mutane takwas cikinsu har da matan aure biyu.
Sai dai, dukkan mutanen takwas da aka sace tare da yin garkuwa da su a makon da ya gabata sun samu damar tserewa yayin da ‘yan bindigar ke bacci.
A cewar wata majiya da ke kauyen, ‘yan bindigar sun fusata ne shine suka sake dawowa sakamakon tserewar mutanen tare da kama wasu a matsayin madadinsu.
KU KARANTA: Kotu ta tura wani gidan yari saboda yi wa Gwamna Badaru ƙazafi a Facebook
A kwanakin baya ne Farfesa Zulum ya ce duk da kisan manoma 43 da mayakan kungiyar Boko Haram su ka yi a Zabarmari, tsaro ya karu a jihar a karkashin mulkin shugaban kasa, Muhammadu Buhari.
Farfesa Zulum, ya bayyana hakan ne ranar Lahadi yayin da ya karbi bakuncin kungiyar dattijan arewa a karkashin jagorancin shugabanta, Ambasada Shehu Malami, da kuma sakatarenta, Audu Ogbeh.
Hakan na kunshe ne a cikin jawabin da gwamnatin jihar Borno ta fitar ranar Litinin mai taken 'Zulum: Duk da kashe-kashe, shaidu a kasa sun nuna cewa an fi samun zaman lafiya a karkashin mulkin Buhari a Borno.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng