Da duminsa: 'Yan bindiga sun kashe shahararren mafaraucin Adamawa, Mori
- Daya daga cikin mafarautan jihar Adamawa, Young Mori, ya riski ajalinsa a jihar Kaduna da safiyar Talata
- Kamar yadda bayanai suka kammala, masu kiwon shanu ne suka kashe shi bayan sun sha musayar wuta
- Mori yana daya daga cikin mafarautan da aka gayyato tun daga jihar Adamawa don taya yaki da 'yan ta'adda
An kashe shugaban kungiyar mafarauta na jihar Adamawa, Young Mori, a wata musayar wuta da suka yi da 'yan bindiga a jihar Kaduna, kamar yadda iyalansa da wasu majiyoyi suka tabbatar.
Mori yana daya daga cikin mafarautan da aka gayyata don kokarin yaki da 'yan ta'adda a jihohin arewa. Shugaban kungiyar, Salihu Wobkenso, ya tabbatar da faruwar lamarin.
A cewarsa, an kashe Mori ne a Kaduna. "Wannan mummunan labari ne ga mafarautanmu. Young Mori, daya daga cikin jaruman mafarautan jihar Adamawa daga karamar hukumar Guyuk ya riski ajalinsa a jihar Kaduna. Masu kiwon shanu sun kashe shi da safiyar yau."
KU KARANTA: Kotun Saudi ta garkame matar da ta yi fafutukar samarwa mata 'yancin tuka mota a kasar
Wobkenso bai bayar da wani bayani dalla-dalla ba a kan mutuwar, sai dai ya bayyana irin alhinin da jama'a suka shiga sakamakon mutuwar, Premium Times ta wallafa.
KU KARANTA: Daga yi mishi allurar rigakafin korona, tsoho mai shekaru 75 ya sheka lahira a Isra'ila
A wani labari na daban, Daruruwan mazauna kauyukan Shindifu, Kirbutu, Debiro, Shafffa, Tashan Alade da Azare a karamar hukumar Hawul ta jihar Borno sun fara komawa gidajensu don ganin barnar da 'yan Boko Haram suka yi musu a yammacin Asabar.
Mayakan ta'addancin sun kai hari a lokaci daya yankunan kasa da sa'o'i 48 da suka kai hari garin Garkida da ke jihar Adamawa, Vanguard ta wallafa.
Da yawan mazauna karamar hukumar Hawul Kirisitoci ne kuma tana da nisan a kalla kilomita 200 daga Maiduguri.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng