Yayar gwamnan Bayelsa Douye Diri ta rasu a Legas

Yayar gwamnan Bayelsa Douye Diri ta rasu a Legas

- Mutanen Jihar Bayelsa na zaman makoki sakamakon rasuwar Madam Elizabeth Carter, yayar Gwamna Diri na jihar

- Mataimakin gwamnan Bayelsa, Sanata Ewhrudjakpo, ya aike da sakon ta'aziyya ga maigidansa

- Sanata Ewhrudjakpo ya yi addu'ar Allah ya jikan wadda ta rasu ya kuma cigaba da kare iyalan wanda aka yi wa rasuwar

Gwamnan Jihar Bayelsa, Douye Diri, ya rasa yar uwarsa mai suna Madam Elizabeth Carter kamar yadda rahotanni suka bayyana.

Wannan na dauke ni cikin sakon ta'aziyya da mataimakin gwamnan jihar, Sanata Lawrence Ewhrudjakpo ya aike wa maigidansa gwamna Diri a daren ranar Laraba 30 ga watan Disambar 2020 kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Yayar gwamnan Bayelsa Doure Diri ta rasu a Legas
Yayar gwamnan Bayelsa Doure Diri ta rasu a Legas
Source: UGC

DUB WANNAN: Zamfara: 'Yan bindiga sun kashe dillalin da shanu saboda yaki siyan shanun sata

A sakon ta'aziyyar da mataimakinsa na bangaren kafafen watsa labarai, Doubara Atasi, ya fitar, Sanata Ewhrudjakpo ya ce ya yi bakin cikin rasuwar 'yar uwar gwamnan a Jihar Legas.

Ewhrudjakpo ya kuma mika sakon ta'aziyya ga iyalai, da sauran yan uwa da abokan wacce ta rasu, inda ya ce rashin dan uwa abu ne mai matukar ciwo.

Mataimakin gwamnan ya kwantar wa mai gidan hankali da tunatar da shi cewa "mutuwa riga ce da ke wuyan kowanne mahaluki" duk da cewa rashin dan uwa abu ne mai ciwo.

KU KARANTA: Gwamnatin Najeriya za ta ceto dan Najeriya da Saudiyya ta yanke wa hukuncin kisa

Ya kuma yi addu'ar ubangiji ya jikan wadda ta rasu ya bawa iyalanta hakurin jure rashin marigayiya Elizabath Carter.

A wani labarin daban, Sanata Elisha Abbo mai wakiltar mazabar Adamawa Ta Arewa a Majalisa ta 9 ya tabbatar da cewa zai yi takarar gwamna a Jihar Adamawa a shekarar 2023, The Punch ta ruwaito.

Abbo wanda ya bayyana hakan a Ganye kuma ya ce ya fice daga jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP, ne saboda jam'iyyar ta mutu.

A wurin gasar gano zakarun 'yan kwallon kafa da sashin matasa na kungiyar yakin neman zabensa ta shirya, mai suna Sanata Ishaku Abbo Ambassadors, (SIA Ambassadors), Abbo ya ce zai yi takarar kujerar gwamna a Adamawa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel